✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPOB: ’Yan bindiga sun fille kan dan majalisa a Anambra

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Echeng Echeng, ya bayyana kisan dan majalisar a matsayin abin kunya ga tsoron kasa.

Wasu ’yan bindiga da ake zargi ’yan kungiyar awaren nan ce ta Biyafara (IPOB), sun fille kan Okechukwu Okoye, dan majalisa mai wakiltar al’ummar Gwamna Charles Soludo a Majalisar Dokokin Anambra.

Mista Okoye, wanda ke wakiltar mazabar Aguata 2 a Jihar Anambra, an sace shi ne tare da wani hadiminsa, Cyril Chiegboka, a ranar Lahadin makon jiya a hanyar Aguluzigbo da ke Karamar Hukumar Anaocha ta jihar.

An ce an jefar da kansa ne a wani wurin shakatawa na Chisco da ke Amichi, a Karamar Hukumar Nnewi ta Kudu a ranar Asabar, kwanaki shida bayan sace shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Asabar.

Ya ce daga baya an tsinci gawar dan majalisar a kan titin Ideani da ke unguwar Nnobi ta Karamar Hukumar Idemili ta Kudu.

Sai dai bai bayyana komai kan makomar haidmin dan majalisar Cyril Chiegboka ba, amma akwai alamun mai yiwuwa shi ma an kashe shi.

Kakakin ’yan sandan ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Echeng Echeng, ya bayyana kisan dan majalisar a matsayin “abin kunya ga tsoron kasa”

Mista Echeng ya kuma jajantawa ’yan uwa da abokanan dan majalisar tare da ba da tabbacin cewa ’yan sanda za su zakulo wadanda suka kashe shi.

Wani faifan bidiyo da ya dauki kan da aka jefar a wurin shakatawa ya bazu a shafukan sada zumunta daban-daban.