✕ CLOSE Kiwon LafiyaRa’ayoyiRa'ayin AminiyaRahotoAminiyar KurmiHotunaGirke-GirkeSana'o'iKimiyya da Kere-Kere

Iran na da take-taken kai mana hari – Saudiyya

Amurka ta ce a shirye take ta tallafa wa Saudiyya kan lamarin

Kasar Saudiyya ta shaida wa Amurka cewa take-taken kasar Iran sun nuna cewa tana kokarin kai mata hari.

Sai dai da take mayar da martani a kan lamarin, Amurka ta ce ta damu matuka da rahotannin, kuma shirye take ta dauki matakin da ya dace a kan Iran.

Majalisar Tsaron Amurka ta fada a cikin wata sanarwa ranar Talata cewa, “Wannan barazanar abar damuwa ce matuka, kuma za mu kasance tare da Saudiyya ta bangaren soji da kuma bayanan sirri. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen taimaka wa kawayenmu a wannan yanki.”

Sai dai tsakanin Saudiyyar da Iran har yanzu babu wanda ya magantu a kan matsayin na Amurka.

Jaridar Wall Street Journal ta Amurka ce dai ta fara rawaito bayanin sirrin da Saudiyya da aike wa Amurka ranar Talata.

Iran dai ta sha zargin cewa Saudiyya da sauran abokan gabarta su ne kanwa uwar gami a zanga-zangar kin jinin gwamnatin da ake gudanarwa a kasarta tun a tsakiyar watan Satumban da ya gabata.

Kazalika, a watan Oktoban da ya wuce, Kwamandan Rundunar Tsaro ta Musulunci ta kasar Iran, ya gargadi Saudiyya da ta janye jikinta daga yada rahotannin zanga-zangar da take yi a wasu tashoshinta na talabijin.

Shi ma Kakakin Sashen Harkokin Wajen Amurka, Ned Price ya ce kasarsa ta damu matuka da abin da ke shirin faruwa tsakanin kasashen biyu, kodayake bai yi karin haske ba a kai.