✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta fara gwajin rigakafin COVID-19 da ta samar a cikin gida

Za a yi wa ’yan kasar miliyan 83 allurar rigakafin COVID-19

Kasar Iran ta fara gwajin allurar rigakafin cutar COVID-19 da ta sana’anta a cikin gida.

A ranar Talata aka yi wa wasu mutum biyu allurar rigakafin mai Coviran Barekat, a gaban Ministan Lafiyar kasar.

Karin wasu mutum 56 kuma za su karbi allurar, wanda shi ne matakin farko na gwajin rigakafin kafin a fitar da sakamako a cikin wata daya.

Shugaba Hassan Rowhani ya ce Iran za ta yi amfani da rigakafin COVID-19 da aka sana’anta a kasashen waje da kuma na cikin gida.

Iran na fama da matsala wajen yin odar rigakafin cutar daga waje, saboda takunkumin da Amurka ta sanya mata, wanda ya sa ba ta iya yin huldar banki wajen yin cinikayya da wasu kasashe.

Duk da haka, Babban Bankin Iran ya ware akalla Dala miliyan 245 domin shigo da rigakafin daga kasashen waje.

Kawo yanzu yawan mutanen da ke dauke da cutar COVID-19 a Iran ya ragu sakamakon dokar kullen da gwamnatin kasar ta tsaurara.

Sai dai kuma a kullum kimanin mutum 6,000 ne ke kamuwa da ita, 120 kuma take yin ajalinsu a kasar.

Daga lokacin da cutar ta fara bulla zuwa yanzu, ta yi kashe mutum 54,000 daga cikin mutum miliyan 1.2 suka kamu da ita a Iran.

Yanzu kasar ta fara kokarin samar da rigakain cutar ga ’yan kasar miliyan 83 a watar Maris na 2021.