✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta harba makamai masu linzami cikin Iraqi

An kai harin ne kan Ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin Erbil

Jami’an tsaron Iran sun ce su ne suka harba wasu makamai masu linzami a birnin Kurdawa na Erbil da ke Arewacin kasar Iraqi, kamar yadda kafafen yada labaran Iran din suka tabbatar.

A cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Asabar, dakarun na Iran sun ce sun harba makaman ne a yunkurinsu na samun wata cibiya ta Isra’ila a kasar ta Iraqi.

Sanarwar ta kuma yi gargadin cewa duk wani yunkurin mayar da martani daga Isra’ilan zai fuskanci mummunan mataki.

Isra’ila dai kashe dakarun tsaron Iran biyu na IRGC a farkon makon nan a Siriya, wacce kawa ce ta kurkusa ga Iran din.

Tun da farko dai hukumomin birnin na Erbil sun ce makaman da dama da aka jefa daga wajen kasar ta Iraqi sun fada birnin, inda Gwamnan yankin, Omed Khoshnaw, ya ce harin na ta’addanci ne a kan Ofishin Jakadancin Amurka a kasar.

A cewar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Iraqi, makaman sun yi illa ne kawai ga sabon ginin Ofishin Jakadancin, in ban da wani farar hula daya da ya samu rauni.

Sashen Harkokin Waje na Amurka ya bayyana harin a matsayin na ba-zata, amma ya ce babu Ba’amuriken da ya shafa ko kuma ginin gwamnatin kasar da ke birnin na Erbil.

Gidan talabijin din gwamnatin Iraqi ya rawaito cewa sashen yaki da ta’addanci na yankin na cewa makamai 12 da aka harba daga wajen kasar ne suka fada wa birnin na Erbil.