✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta ki karbar kyautar alluran Kwarona da aka yi a Amurka

Iran na shigo da riga-kafi daga kasashen Yamma, amma ban da Amurka da Birtaniya.

Kasar Iran mayar da alluran riga-kafin Kwarona dubu 820 da kasar Poland ta ba ta saboda an sarrafa alluran ne a kasar Amurka.

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ne ya ruwaito haka daga gidan talabijin na Iran a ranar Litinin da ta gabata.

Gidan talabijin din ya ruwaito Mohammad Hashemi, wani jami’i a Ma’aikatar Lafiya ta Iran yana cewa kasar Poland ta kuma ba Iran kimanin alluran rigakafin miliyan daya da aka samar da su a Sweden na AstraZeneca.

“Sai dai lokacin da alluran suka iso Iran sai muka gano daga cikinsu dubu 820 an shigar da su zuwa Poland ne daga Amurka,” inji shi.

Hashemi ya ce “Bayan tuntubar Jakadan Poland a Iran an yanke shawarar a mayar da alluran.”

Shugaban Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda shi ne ke yanke hukunci ka dukkan al’amuran da suka shafi kasar a shekarar 2020 ya ki amincewa a shigar da alluran riga-kafi daga Amurka ko Birtaniya a kasar inda ya bayyana su da “haramtattu.”

A yanzu Iran tana shigo da alluran riga-kafi daga sauran kasashen Yammacin Turai amma ban da Amurka da Birtaniya.

Cutar Kwarona dai ta hallaka mutum dubu 135, a Iran kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana, inda ta zamo kasar da cutar ta fi hallaka mutane a Gabas ta Tsakiya.

Ta ce fiye da kashi 90 cikin 100 na mutanen kasar da suka haura shekara 18 sun yi allurar riga-kafin cutar, inda kashi 37 suka yi riga-kafin sau uku.