✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta rataye mutum na 2 kan zanga-zangar kin jinin gwamnati

Mutum na biyu ke nan da aka zartar wa hukuncin kisa bayan barkewar zanga-zangar kin jinin gwamnatin Musuluncin Iran

Gwamnatin Iran ta rataye Majidreza Rahnavard mutumin da ta tsare kan kisan jami’an tsaro a tarzomar kin jinin gwamnatin  Musulunci da ke gudana a fadin kasar.

Mutum na biyu ke nan da aka zartar wa hukuncin kisa bayan barkewar zanga-zangar kin jinin gwamnatin Musuluncin Iran.

Gwamnatin kasar Iran ta fitar a wani bidiyo a ranar Litinin da ke nuna wani mutum, wanda ta ce Rahnavard ne, a lokacin da yake daba wa wasu jami’an tsaro biyu wuka ya kashe su, sannan ya tsare.

Rataye Rahnavard  a ranar Litinin na zuwa ne kasa da wata guda bayan tsare shi kan zargin kashe jami’an tsaron, a zanga-zangar da ake gudanarwa a kasar, kan zargin jami’an tsaro da wuce gona da iri.

Ana ganin matakin gwamnatin a matsayin yunkurin hanzarta kashe mutanen da take tsare da su kan zanga-zangar kin jinin gwamnatin Musulunci da ke jagorantar kasar.

’Yan gwagwarmaraya na zargin an yanke wa akalla mutum 12 hukuncin kisa bayan zaman kotun da aka gurfanar da su a sirrance.

Masu rajin kare hakkin dan Adam da ke sa ido kan tarzomar sun ce an kashe akalla mutum 500 baya ga wasu 18,200 da ake tsare da su tun bayan fara zanga-zangar a watan Satumba.