✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta rufe jarida kan alakanta Shugaban Addini na Kasar da talauci

Hukumomin a kasar Iran sun rufe wata jarida da ta buga wani hoto a shafinta na farko da ke nuna hannun Shugaban Addini na kasar…

Hukumomin a kasar Iran sun rufe wata jarida da ta buga wani hoto a shafinta na farko da ke nuna hannun Shugaban Addini na kasar Ayatollah Ali Khamenei da jawo talauci a kasar.

Daukar matakin na zuwa ne a daidai lokacin da mutanen kasar suke ci gaba da nuna bacin ransu kan kara tabarbarewar tattalin arziki.

Kamfanin Dillancin Labarai na gwamnatin kasar Mehr ya ce hukumar da ke sanya ido kan gidajen jaridu ta rufe jaridar Kelid mai fitowa kullum bayan ta buga labari mai taken “Miliyoyin Iraniyawa na rayuwa cikin kangin talauci.”

A karkashin labarin, akwai zanen hoton hannun hagu na mutum rike da alkalami ya zana jan layi da ke nuna irin talaucin da mutane suke ciki.

Hoton ya yi kama da na Khamenei yana rubutu a kan takarda da hannunsa na hagu da kuma fitaccen zobensa a daya daga cikin yatsunsa.

Ya rasa hannunsa na dama a wani harin bam ne a 1981.

Kamfanin Dillancin Labaran Iran (IRNA), ya tabbatar da rufe jaridar Kelid ba tare da bayyana dalilin yin haka ba.

Ba a samu jin ta bakin jaridar Kelid ba, yayin da shafinsu na Intanet ya yi layar zana. Iran wacce tattalin arzikinta ya dade yana fuskantar matsala bayan juyin-juya-halin Musulunci na 1979, ta kara fuskantar matsin lamba lokacin da tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta kulla da kasashen duniya a shekarar 2018.

A shekarar 2015 da aka kulla yarjejeniyar nukiliyar, ana canja Dalar Amurka daya a kan Riyal din Iran dubu 32, amma a yanzu ana canja Dala daya da Riyal din Iran dubu 281 da 500.

Kuma takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasar yana ci gaba da durkusar da tattalin arzikinta, tare da haifar da hauhawar farashin kayayyaki da ke jefa talakawan Iran a cikin matsi.

Hakan ya sa mutane sun rika rage yawan nama da madarar da suke saye wata-wata. A kasar Iran gidajen rediyo da talabijin duk mallakar gwamnati ce, sai dai jaridu da mujallu mutane masu zaman kansu kan iya mallakarsu.

Sai dai ’yan jaridar Iran suna fuskantar cin zarafi a-kai-a-kai da kuma barazanar kama su a cewar kungiyoyin kare hakkin ’yan jarida.

Kwamitin Kare Hakkin ’Yan jarida na Duniya, ya yi kira ga Iran ta gaggauta janye matakin da ta dauka na rufe jaridar. Sherif Mansour, jami’in kula da Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka na kwamitin, ya ce “Bayanai na gaskiya a bayyane suke a kan yadda al’amuran yau da kullum suke kara ta’azzara wanda hakan na da matukar muhimmanci ga al’ummar Iran.”

“Dole ne hukumomin Iran su kyale jaridar Kelid ta ci gaba da aiki nan take tare da dakatar da duk wani yunkuri na yi wa kafafen yada labarai zagon kasa.