✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta zargi Isra’ila da mai mata hari

Iran ta zargi Isra'ila da kai mata hari da jirage marasa matuka a wata masana'antar soji.

Iran ta zargi Isra’ila da kai mata hari da jirage marasa matuka a wata masana’antar soji.

Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeid Iravani, ya shaida mata cewa bincikensu ya gano cewa gwamnatin Isra’ila ce ta kai harin a lardin Isfahan.

A wasikarsa ga Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya kuma zargin kalaman barazanar jami’an gwamnatin Isra’ila na kai hari kan kadarorin Iran.

Sai dai, Iravani bai yi karin bayani kan zargin ba, amma yana “Bukatar Kwamitin Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya ya la’anci wannan abin kyamar da Isara’ila ta aikata.

“Sannan ta tilasta mata bin dokokin kasa da kasa da kuma shirye-shiryenta masu hadari a yankin.”

An shafe shekaru ana yakin bayan fage tsakanin Isra’ila da Iran wadda ke zargi da kai hare-haren rusa shirinta na nukiliya, da hadin bakin Amurka.

Iravani ya ce, “Iran na da cikakken karen kanta a matsayin kasada kuma mayar da martani ga duk wata barazana daga Isra’ila, duk lokacin da hakan ta kama.