✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Iran za ta rufe iyakarta da Iraki saboda tsoron yaduwar COVID-19

Hukumomin kasar Iran sun ce za su rufe kan iyakarsu da Iraki ta yankin Khuzestan saboda tsoron yaduwar sabon nau’in COVID-19.

Hukumomin kasar Iran sun ce za su rufe kan iyakarsu da Iraki ta yankin Kudu maso Yammacin Khuzestan saboda tsoron yaduwar sabon nau’in cutar COVID-19.

Kamfanin Dillancin Labaran Dalibai na Kasar (ISNA) ya rawaito cewa Gwamnan yankin na Khuzestan, Qassem Dashtaki ne ya sanar da matakin kasar ranar Alhamis.

A cewarsa, “Daga ranar Asabar, Iran za ta rufe kan iyakokinta na Shalamcheh da na Chazzabeh har tsawon mako daya saboda takaita shigar fasinjoji.

“A tsawon wannan lokacin, hukumomin kasar Iran za su samar da kayayyakin gwajin cikin gaggawa da kuma wuraren killace mutane na wucin gadi a kan iyakokin,” inji shi.

Hukumomin lafiyar kasar ta Iran dai sun yi gargadi kan sake barkewar cutar a kasar inda suka ce sun dauki tsauraran matakai domin takaita bazuwarta.

Ma’aikatar Lafiyar kasar dai ta ce a iya ranar Alhamis kawai, mutane 8,066 suka sake kamuwa da cutar, lamarin da ya kawo adadin masu dauke da ita a kasar zuwa 1,550,142.

Kazalika, akalla mutum 59,264 ne suka rasu, kamar yadda kakakin ma’aikatar, Sima Lari ta tabbatar yayin jawabin da take yi kan annobar kullum a kasar.