✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Iska mai karfi ta kashe mutum 2 ta rushe gidaje 1,500 a Katsina

Wata iska mai karfin gaske tare da mamakon ruwan sama ta yi sanadiyar mutuwar mutum biyu, ta kuma lalata gidaje sama da 1,500 a Kananan…

Wata iska mai karfin gaske tare da mamakon ruwan sama ta yi sanadiyar mutuwar mutum biyu, ta kuma lalata gidaje sama da 1,500 a Kananan Hukumomin Faskari da sabuwa a Jihar Katsina.

Mai magana da yawun hukumar ba da agaji ta Jihar Katsina, Umar Muhammed, ya ce ruwan sama mai karfin gaske da ya shafe sama da sa’a biyar yana kwarara a Karamar Hukumar Bindawa ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu a ranar Litinin 26 ga watan Yuli.

Ya kara da cewa a garin Bindawa kadai gidaje 400 ne suka salwanta, gidaje sama da 800 kuma a Faskari, sai wasu akalla 300 da aka rasa a Karamar Hukumar Sabuwa.

Umar ya kara da cewa hukumar na -shirye shiryen kai wa al’ummar da lamarin ya shafa dauki.