✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iska mai karfi ta rusa gidaje 300 a Kebbi

Akalla gidaje 300 ne guguwa ta lalata a jihar Kebbi sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka ranar Juma’a. Rahotanni sun nuna cewar guguwar…

Akalla gidaje 300 ne guguwa ta lalata a jihar Kebbi sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka ranar Juma’a.

Rahotanni sun nuna cewar guguwar ta fi kamari ne a yankunan Badariya, barikin ‘yan sanda, Bayan-Kara da kuma wani bangare na Gesse III da ke Birnin Kebbi.

Wasu daga cikin wadanda iftila’in ya shafa sun shaida cewa sun yi matukar kaduwa da mawuyacin halin da suka tsinci kansu sakamakon guguwar, suna masu cewa zai yi wuya a iya tantance yawan barnar da ta yi zuwa yanzu.

Malam Isyaku Mohammed, wani mazaunin yankin ya yi hasashen cewa akalla gidaje 50 guguwar ta lalata.

“Ina ganin idan mutum ya ce guguwar nan ta lalata akalla gidaje 50 a sassa da dama na Birnin Kebbi bai yi kuskure ba.

“Mun dauki wannan iftila’in a matsayin jarrabawa daga Allah da ba wanda ya isa ya kauce wa”, inji Mohammed.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta kawo wa al’ummar yankunan tallafin gaggawa don rage radadin barnar da guguwar ta haifar.

Shi kuwa a nasa bangaren, wani wanda guguwar ta yi wa barna mai suna Isaac Musa ya ce guguwar ta taso ne da yammacin ranar Juma’a kuma ta yi barna a yankunan.

Ya yi kira ga gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran al’umma mawadata da su taimaka wa mutanen da iftila’in ya raba da muhallansu.

Da ya ke amsa tambayoyin ‘yan jarida, shugaban karamar hukumar Birnin Kebbi, Aminu Ahmad Magatakarda ya ce ba a sami rasa ran ko da mutum daya ba sakamakon guguwar.

To sai dai gwamatin jihar a wata sanarwa ta bakin kakakin gwamnan jihar, Abubakar Mu’azu-Dakingari ta ce tuni Gwamna Atiku Bagudu ya kai ziyarar gani-da-ido a yankunan da lamarin ya shafa ranar Asabar.

Gwamnan ya ce suna aikin gano yawan gidajen da lamarin ya shafa da kuma irin girman barnar tare da alkawarin tallafawa.

Rahotanni dai sun nuna cewa guguwar ta karairaya turakun wutar lantarki da dama musamman a yankin Badariya, lamarin da ya jefa mutanen yankin cikin duhu.