✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila: An kama masu zanga-zangar adawa da Netanyahu

'Yan sanda goma sha daya sun ji rauni yayin arangamarsu da masu zanga-zangar.

’Yan sanda sun kame mutane da dama tare da jikkata wasu a ranar Asabar bayan da wasu suka fito zanga-zangar adawa ga Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Dubun-dubatar masu zanga-zanga sun taru a gaban gidan Netanyahu da ke birnin Urshalima, baya ga zanga-zangar da aka gudanar a wasu biranen kasar.

Netanyahu dai na fuskantar tuhumar aikata cin hanci da rashawa tun watan Mayun da ya gabata.

Ko a watannin da suka gabata sai da ’yan kasar ta Isra’ila suka yi zanga-zanga a kansa.

Sai dai a yayin zanga-zangar an samu barkewar fada tsakanin magoya bayansa, a wurare daban-daban inda ’yan sanda suka kame mutane dama.

Jami’ai a hedikwatar ’yan sanda ta Urushalima,  sun yi artabu da masu zanga-zangar adawa da buge wani Ba’Amurke dan shekara 16 mazaunanin Isra’ila, a lokacin da yake kokarin tserewa daga hannun ’yan sandan.

Jaridar the Times da ke Isra’ila da wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa matashin a baya ya jefi Falasdinawa da duwatsu.

Rundunar ’yan sandan ta sanar da cewa an yi wa jami’anta 11 rauni, sannan sun cafke 11 daga cikin wanda aka yi arangamar da su.