✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila da kungiyar Falasdinawa sun tsagaita wuta

Yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Falasdinawa ta Islamic Jihad ta fara aiki a cikin dare kafin wayewar garin Litinin.

Yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar Falasdinawa ta Islamic Jihad ta fara aiki a cikin dare kafin wayewar garin Litinin.

Tun da farko Isra’ila da Kungiyar Falasdinawa sun sanar da cewa tsagaita bude wuta za ta fara aiki a cikin dare, ranar Lahadi.

Ofishin Fira Ministan rikon kwarya na Isra’ila, Yair Lapid, ya tabbatar cewa tsagaita bude wuta da ’yan kungiyar Jihadin na Falasdinu za ta fara aiki da karfe 11:30 na dare agogon GMT a ranar Lahadi.

Gabanin haka, kungiyar ta sanar da amincewarta da matakin a tsakanin bangarorin biyu.

Ana kyautata zaton tsagaita wutar na iya kawo karshen rikicin kan iyaka tsakanin Isra’ila da Falasdinawa mafi muni tun bara.

Yadda sabon tashin hankalin ya faru

Isra’ila ta fara kai samamen soji mai lakabin “Breaking Dawn,” a ranar Juma’a.

Ya zuwa yanzu, hare-haren da ta kai ta sama sun kashe wasu manyan ’yan kungiyar Islamic Jihad, ciki har da manyan kwamandojin biyu — Khaled Mansour da Tayseer al-Jabari.

Rundunar sojin Isra’ila na zargin Mansour da al-Jabari na shirin kai hare-haren ta’addanci.

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce mutane 41 ne suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila ya zuwa yanzu, ciki har da kananan yara da dama.

Isra’ila ta ce an kashe yaran ne sakamakon harba makamin roka da kungiyar ta yi.

A cewar hukumomin Gaza, akalla mutane 311 ne suka samu raunuka.

Mayakan Falasdinawa sun harba daruruwan rokoki a garuruwan Isra’ila da suka hada da Tel Aviv da Ashkelon.

Ya zuwa yanzu, wasu ’yan Isra’ila biyu sun sami raunuka yayin da fararen hula suka tsere zuwa maboyar karkashin kasa saboda tsoron rokokin Falasdinawa.

Isra’ila ta kuma ce hare-haren atilaren Falasdinawa sun lalata mashigar kan iyakarta da Gaza Erez.

Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da sauran mambobin kasashen duniya sun yi kira da a sassauta tashin hankalin.

Kungiyar Hamas mai kishin Islama da ke mulki a Gaza ta yi watsi da wannan rikici.

EU da Amurka dau sun na kallon Hamas da Islamic Jihad a matsayin kungiyoyin ta’addanci masu muradun kawar da Isra’ila.