✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila da UAE sun kulla yarjejeniyar kawance

Falasdinawa sun ce kawancen da Hadaddiyar Daular Larabawa ta shiga babbar kasada ce

A wani mataki mai cike da tarihi, kasashen Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun cimma yarjejeniya tare da amincewar su dawo da huldar jakadanci a tsakaninsu.

Sai dai Falasdinawa sun bayyana matakin a matsayin babban yankan baya gare su.

Yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar a yammacin Alhamis, ya ce Isra’ila ta amince ta dakatar da mamayar da take a gabar yammacin Kogin Jordan har zuwa wani lokaci.

UAE ita ce kasar Larabawa ta uku bayan Masar da Jordan da ta sanar da dawo da hulda da Isra’ila ka’in da na’in.

— Yadda aka kulla yarjejeniyar

An kai ga cimma yarjejeniyar ne bayan wata doguwar tattaunawa a kwanan nan da Amurka ta jagoranta.

Hakan kuma na zuwa ne bayan wata tattaunawa ta wayar salula tsakanin Shugaba Trump na Amurka, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da Sarkin Abu Dhabi, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan da safiyar Alhamis.

Ana sa ran wakilan kasashen biyu su hadu cikin makonni masu zuwa domin rattaba hannu a kan bangarorin da suka shafi zuba jari, yawon bude ido, sufurin jiragen sama na kai tsaye, sadarwa da kuma harkar tsaro.

Da yake jawabi ga ‘yan jaridar a Fadar White House, Trump ya ce, “Yanzu da aka riga aka samu wannan gagarumar nasarar, ina fatan ganin karin kasashen Larabawa da na Musulmai su ma su bi bayan UAE”.

— Falasdinawa sun yi watsi da yarjejeniyar

To sai dai tuni kungiyoyin Falasdinawa su ka yi watsi da yarjejeniyar, da cewa babu abun da za ta tsinana musu.

Jam’iyyar Hamas ta bayyana alakar a mtsayin ci gaban mai hakan rijiya kuma wanda da ba zai amfani kowa ba sai Isra’ilan.

Ita kuwa takwararta ta Fatah bayyana sabon kawancen ta yi a matsayin wani yunkuri na yin amfani da UAE domin a kara samun damar danne ta.

Masana huldar diflimasiyya da dama na ganin cewa babu wata rawa da wannan yarjejeniyar za ta taka wajen samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.