✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta haramta wa Yahudawa zuwa Amurka saboda Omicron

Ba kasafai dai kasar ke daukar irin wannan matakin a kan Amurka ba.

Kasar Isra’ila ta sanya Amurka a jerin kasashen da ta haramta wa’yan kasarta shiga saboda karuwar barazanar samfurin COVID-19 na Omicron.

Majalisar Ministocin kasar dai, wacce ta yi aiki da shawarwarin Ma’aikatar Lafiyar kasar a ranar Litinin ta sanya kasashen Amurka da Italiya da Belgium da Jamus da Hungary da Maroko da Portugal da Kanada da Switzerland da kuma Turkiyya, a jerin kasashen da ta hana jiragenta tashi zuwa can.

Matakin dai, wanda ba kasafai kasar ke daukar irinsa a kan Amurka ba na zuwa ne a daidai lokacin da yawan sabbin masu kamuwa da COVID-19 ke dada karuwa a Isra’ila, duk kuwa da irin kyakkyawar dangantakar diflomasiyyar da ke tsakanin kasashen biyu.

Hakan dai na nufin Amurka za ga bi sahun kasashen Turai da ma na wasu Nahiyoyin da Isra’ilan ta haramta wa ’yan kasarta zuwa, yayin da wadanda za su dawo daga can dole a killace su tsawon lokaci.

Ana sa ran dai nan ba da jimawa ba kwamitin Majalisar Ministocin ya ba d a amincewa ta karshe a kan matakin.

Da zarar an amince da hakan dai, matakin zai fara aiki ne daga tsakar daren ranar Laraba.