✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta harba makami mai linzami filin jirgin saman Syria

Harin ya tilasta dakatar da sauka da tashin jirage a filin

Kafar yada labaran gwamnatin Syria ta tabbatar da kai harin makami mai linzami da Isra’ila ta kai mata wanda ya ragargaza filin jirgin da ke babban birninta, wato Damascus.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Sufurin kasar ta fitar a karshen mako, ta ce an dakatar da zirga-zirga a filin jirgin bayan harin ranar Juma’ar da Isra’ila ta kai mata.

“Sauka da tashin jirgi ya tsaya cak daga yau, har sai lamura sun daidaita. Sakamakon harin Isra’ila, muna tattaunawa da ma’aikatan da ke kula da shawagin jiragen sama kan hakan,” a cewar sanarwar.

Kafar yada labaran kasar ta rawaito cewa jiragen yakin Isra’ila dai sun yi wa filayen luguden makamin ne da karfe 1:20 na safiya a agogon GMT ranar Juma’a.

Tun daga shekara ta 2011 dai kasar ta Syria ke shan hare-hare daga Isra’ila, inda suka fi mayar da hankali kan Sojojin gwamnati, da mayakan Iran da Hezbollah da ke dafa wa kasar.

Duk da cewa Isra’ilan ba ta cika magana kan hare-harenta ba, a wannan karon ta ce matakin dole ne la’akari da yadda ta ce kasar Iran ke shisshigin matsarta.