✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta kashe Falasdinawa 24 a sabbin hare-hare kan Zirin Gaza

Isra'ila ta ce akwai yiwuwar ta shafe mako daya tana kai hare-haren

Wasu sabbin hare-hare da Isra’ila ta kaddamar a yankin Zirin Gaza ta sama sun yi sanadin kisan kananan yaran Falasdinawa da dama da kuma wani babban Kwamandan wata kungiya mai dauke da makamai.

A cikin wata sanarwa da kungiyar masu dauke da makaman mai suna Islamic Jihad ta fitar ranar Lahadi, ta tabbatar da kisan Khalid Mansur, Kwamandanta na Kudancin Zirin Gaza a harin na Isra’ila na ranar Asabar.

Khalid dai shi ne na biyu daga cikin manyan jagororin kungiyar da aka hallaka tun bayan kaddamar da hare-haren da Isra’ila ta yi ranar Juma’a.

A ranar farko dai jiragen yakin na Isra’ila sun kashe Taysir Al-Jabari, Kwamandan kungiyar a Arewacin Gaza.

Isra’ila dai ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar ta shafe tsawon mako guda tana ruwan wuta a yankin, kuma tuni ta lalata gidaje da sansanonin ’yan gudun hijira masu yawa.

Kungiyar Hamas da ke mulkin Zirin na Gaza ta ce akalla kananan yara hudu ne aka kashe a daya daga cikin hare-hare kan wani sansanin gajiyayyu na Jabaliyya ranar Asabar.

Kungiyar dai ta zargi Isra’ilan da kisan, kodayake sojojinta sun musanta hakan, tare da alakanta ta da fashewar wata roka da kungiyar Jihadin ta jefa mata amma ta fashe a yankin.

Kisan na baya-bayan nan dai ya kawo adadin yaran da aka kashe zuwa daga ranar Juma’a zuwa shida, yayin da jimlar mutanen da aka kashe ya kai 24.

Kazalika, wasu mutum 204 kuma sun jikkata, kamar yadda Ma’akatar Lafiyar Zirin ta tabbatar.

A nasu bangaren kuwa, mayakan Falasdinawa sun harba rokoki sama 400, kodayake Isra’ila ta ce ta kakkabo akasarinsu, kuma ba a sami asarar rayuka ba.

Rikicin dai ya kara fargabar sabon rikici tsakanin bangarorin guda biyu, watanni 15 bayan rikicin da ya shafe tsawon wata daya ya kai ga kisan sama da mutum 260.