✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta rufe hanya daya tilo da Falasdinawa ke bi don shiga Zirin Gaza

Matakin na zuwa ne bayan Isra’ila ta zargi Hamas da harba mata rokoki

Falasdinawa na ci gaba da yin Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na rufe mashigarta daya tilo ga ma’ikatan Falasdinawan da ke zuwa daga Zirin Gaza.

Sun dai bayyana matakin na Isra’ila a matsayin ‘tsattsauran hukunci’ ga mazauna yankin da ke fama da talauci wadanda suka kai miliyan biyu kuma suke rayuwa karkashin shingen Isra’ila da Masar na kusan shekara 15.

 

Matakin da aka sanar a ranar Asabar, ya zo ne bayan da sojojin Isra’ila suka zargi Kungiyar Hamas mai dauke da makamai da ke mulkin Zirin na Gaza da harba rokoki uku a cikin Isra’ila da yammacin  Juma’a.

Hakan kuma na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar rikici a watan Ramadan mai alfarma da Musulmi ke ibada.

Daya daga cikin rokokin ta fada a sararin Subuhana a cikin Isra’ila, yayin da dayar kuma ta fada cikin yankin Falasdinawa, inji rundunar sojin Isra’ila, ba tare da bayar da cikakken bayani kan ta ukun ba.

A farkon makon nan ne, sojojin Isra’ila sun ce an harba rokoki guda hudu daga Gaza, amma na’urorin tsaron sama sun dakile su.

“Bayan rokoki da aka harba zuwa yankin Isra’ila daga zirin Gaza a daren Juma’a da ta gabata, an yanke shawarar cewa, ba za a ba da izinin shiga Isra’ila ga ’yan kasuwa da ma’aikata na Gaza ta mashigar  Erez a ranar Lahadi mai zuwa ba,” kamar yadda wani  sashen Ma’aikatar Tsaro da ke da alhakin kula harkokin Falasdinawa ya fitar da sanarwar.

Kungiyar Ma’aikatan Gaza ta ce, rufe mashigar zai yi matukar illa ga matsin tattalin arzikin da ake fama da shi, inda rashin aikin yi ya kai kusan kashi 50 cikin 100.

Ta ce daukar matakin gabanin hutun bikin karamar Sallah da ake yi a karshen watan Ramadan zai kara radadi ga iyalan da ke fafutukar samun abin kai wa bakunan salati.

Shugaban Kungiyar, Sami Amassi ya ce izinin hakan yin hakan na da wasu alaka ga ma’aikata don dalilai na siyasa, maimakon inganta rayuwarsu.

Mai magana da yawun Hamas, Hazem Wassem ya ce, “matakin na da nufin kara matsa lamba kuma wani nau’i ne na wuce gona da iri da ba za mu amince da shi ba.

“Wannan ba zai yi nasara ba. ’Yan sandan da ke hukunta Falasdinawa a kodayaushe suna nuna gazawa,” kamar yadda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press.

Isra’ila ta kai hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na Zirin Gaza sau biyu a makon jiya, inda sojojin Isra’ilan suka ce jiragen yakinta sun kai hari kan sansanonin da sojoji suke.

An dai yi musayar wuta ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali a masallacin Al-Aqsa da ke gabashin birnin Kudus da Isra’ilan ke mamaye da shi, wanda aka fara a farkon watan Ramadan din nan.

Akalla Falasdinawa 57 ne suka jikkata a ranar Juma’a bayan da sojojin Isra’ila suka kai farmaki kan masallacin tare da kai wa masu ibada hari da harsashin roba da gurneti da kuma harba hayaki mai sa hawaye.

An kuma harba hayaki mai sa hawaye bayan sallar Juma’a, inda ya afkawa Falasdinawa da suke ibada.