✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta saki Bafalasdinen da ya shekara 40 a kurkukunta

An daure Karim Younis sakamakon kashe sojan Isra'ila a 1983.

Kasar Isra’ila ta saki Bafalasdinen da ya fi kowane fursuna dadewa a kurkukunta, wato Karim Younis.

An saki Karim mai shekara 66 ne bayan da ya shafe shekara 40 a kurkukun kasar.

Karim ya fuskanci hukuncin zaman gidan kaso ne sakamakon kashe wani sojan Isra’ila da ya yi a shekarar 1983.

A ranar Alhamis aka sako shi daga kurkukun Hadarim inda ya samu kyakkyawar tarba a wajen jama’ar kauyensu, Ara.

Karim ya shaida wa tashar Aljazeera cewar, sai da aka yawata da shi wurare daban-daban a cikin motocin ‘yan sanda sannan a karshe aka sauke shi a yankin Ranana inda a nan ya samu ya kira ‘yan uwansa da taimakon jama’a.

Bayanai sun ce Karim mutum ne mai muhimmancin ga gwagwarmayar da Falasdiwa ke yin a nema wa kansu ‘yanci.