✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta yi wa kaso 1 cikin 5 na mutanenta rigakafin COVID-19

Ministan Lafiya na Isra’ila, Yuli Edelstein ya ce kasar ta yi wa kaso 20 na mutanen kasar allurar rigakafin cutar COVID-19 a makonni uku

Ministan Lafiya na Isra’ila, Yuli Edelstein ya ce kasar ta yi wa kaso 20 cikin 100 na mutanen kasar allurar rigakafin cutar COVID-19 a makonni uku da fara gangamin yaki da cutar a kasar.

Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, inda ya ce akalla mutane miliyan daya da dubu dari takwas daga cikin sama da mutane miliyan tara da kasar ne suka karbi rigakafin Pfizer-BioNTech.

“Mun kammala makonni ukun farko na yi wa al’ummar kasarmu rigakafin COVID-19 wanda muka yi wa lakabi da farfado da rayuwa cikin gagarumar nasara,” inji ministan.

Firaministan kasar, Benjamin Netanyahu da kuma minista Yuli dai sune na farkon karbar rigakafin a kasar a wani asibiti mai suna Sheba dake kusa da birnin Tel Aviv a ranar 19 ga watan Disambar bara.

Adadin dai ya sa Isra’ila ta kasance kasar da ta fi yi wa mutanen kasarta rigakafin da kaso mafi tsoka a duniya, yayin da take sa ran yi wa dukkan ’yan kasar da suka haura shekaru 16 kafin nan da karshen watan Maris mai zuwa.

Sai dai sakamakon karuwar mutanen da suke kamuwa da cutar a kullum zauwa kusan mutum 800 a kowacce rana tun lokacin da aka sassauta dokar kulle a karo na biyu, a ranar Alhamis kasar ta sake tsaurara dokar a karo na uku.

A wani labarin kuma, Ma’aikatar Lafiyar kasar ta tabbatar da samun nau’uka hudu na sabuwar cutar wacce ta bayyana a Afirka ta Kudu ta bulla a kasarta.

Akalla dai mutane 3,645 ne aka tabbatar cutar ta yi sanadiyyar mutuwarsu tun farkon bullarta kusan shekara daya da ta gabata kenan.