✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta zabi Isaac Herzog a matsayin sabon Shugaban Kasa

Mahaifinsa sabon Shugaban ma ya taba jagorantar kasar daga shekarar 1983 zuwa 1993.

Majalisar Dokokin Isra’ila ta zabi Shugaban ’yan adawar kasar, Isaac Herzog a matsayin sabon Shugaban Kasar.

Mai kimanin shekaru 60 a duniya, Mista Isaac ya samu nasarar zama sabon shugaban ne bayan ya samu kuri’u 87 inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Miriam Peretz wanda tsohon malamin makaranta ne kuma dan gwagwarmaya wanda ya sami kuri’u 26 kacal.

Hakan na nufin Mista Isaac zai karbi ragamar shugabancin kasar daga hannun Reuven Rivlin a ranar 9 ga watan Yulin 2021.

Isaac dai ya kasance jagoran jam’iyyar adawa ta Labour tun shekarar 2013.

Mahaifinsa, Chaim Herzog ma ya taba zama Shugaban Isra’ila daga shekarar 1983 zuwa 1993.

A shekarar 2013, Mista Isaac ya shugabanci Hukumar Bayar da Agaji ta Isra’ila, wacce ita ce ke da alhakin kula da masu son shiga kasar.

Hurumin Shugaban Kasa dai a Isra’ila bai wuce na jeka-na-yi-ka ba, kuma kololuwar matsayi shi ne na damar yi wa fursunoni afuwa da kuma damar kafa gwamnati.

Majalisar kasar dai kan zabi Shugaba ne bayan kowane shekara bakwai a tsarin kada kuri’a na sirri.