✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP da Boko Haram sun kashe mayakansu 30

Mayakan ta'addancin ISWAP da Boko Haram sun kashe kimanin mutum 30 daga cikinsu a musayar wuta

Mayakan kungiyoyin ta’addanci na ISWAP da Boko Haram sun kashe kimanin mutum 30 daga cikinsu, bayan musayar wuta a tsakaninsu.

Akalla mayaka 23 kungiyar Boko Haram ne aka kashe a ranar a Alhamis a harin kwantan bauna da ’yan ISWAP suka kai musu.

Hakan ya faru ne bayan ’yan Boko Haram sun kashe ’yan ta’addan ISWAP 8, ciki har da suka hada da wani kwamandanta da aka fi sani da Kundu, a wani kazamin fada a ranar.

Wani jami’in leken asiri ya shaidawa Zagazola Makama, wani masani kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi cewa, ISWAP ta kashe ’yan Boko Haram 23 ne a farmakin da ta kai wani sansanoninsu da ke Bula Shaidan da Kolori.

Yankunan biyu dai na tsakanin kananan hukumomin Bama da Konduga na Jihar Borno.

Majiyar ta ce, mahara ISWAP a kan babura dauke da muggan makamai karkashin jagorancin Baana Chingori, ne suka mamaye sansanin na Boko Haram suka fatattake su a fafatawar da aka kwashe sa’o’i ana yi.