ISWAP ta kai hari wani kauye a Borno | Aminiya

ISWAP ta kai hari wani kauye a Borno

Sojoji suna kona wani sansanin ISWAP a Jihar Borno ranar 28 ga Afrilu, 2022. (Hoto: Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya).
Sojoji suna kona wani sansanin ISWAP a Jihar Borno ranar 28 ga Afrilu, 2022. (Hoto: Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya).
    Ishaq Isma’il Musa da Olatunji Omirin, Maiduguri

Rahotanni sun bayyana cewa mayakan kungiyar ISWAP mai ikirarin jihadi a Yammacin Afirka, sun kai hari wani kauye da ke kusa da Karamar Hukumar Chibok a Jihar Borno.

Wata majiya ta ’yan sa-kai ta shaida wa Aminiya cewa mayakan sun kai hari kauyen Kautakari da ke da tazarar kilomita 15 tsakaninsa da garin Chibok, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi tare da cinna wa gidaje wuta.

A cewar majiyar, gabanin faruwar wannan hari sai dai mayakan suka tarwatsa wani sasanin dakarun soji a yankin Kada da ke da tazarar kilomita 2 kacal tsakaninsa da kauyen Kautakari.

Majiyar ta ce mayakan sun biyo dare ne ta cikin sahara, inda suka fara harbe-harbe daga kowace kusurwa ba ji ba gani.

“A yanzu haka duk mazauna kauyen da sojoji sun arce cikin daji, wasunsu kuma sun fake a garin Chibok” a cewar majiyar.

Aminiya ta ruwaito cewa wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutterres yake ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Najeriya, inda a ranar Talata ya ziyarci Jihar Borno.

Babban Jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya je Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a ranar Talata inda ya gana da Gwamna Babagana Umara Zulum, da kuma iyalan mutanen da rikicin Boko Haram ya yi sanadin rasa rayukansu.

Kazalika Sakatare Janar din ya gana da shugabannin addinai da na kungiyoyin mata da matasa da kuma shugabanin kamfanoni masu zaman kansu.

Baya ga wadannan mutane da ya gana da su, ya kuma gana da jami’an difilomasiyya da ma wadanda ke sansanonin ’yan gudun hijra a Jihar Borno.