✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ISWAP ta sace motar yaki a sansanin soji a Borno

Mayakan ISWAP sun kashe jami'an tsaro biyu, sun sace wata motar daukar marasa lafiyar sojoji a kusa da Maiduguri

Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe jami’an tsaro biyu tare da sace motar yaki a wani sansanin soji a kusa da Maiduguri, hedikwatar Jihar Borno.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa mayakan da ake zargin ’yan Boko Haram ne dauke da manayn makamai a cikin motoci da babura sun mamaye wuraren binciken jami’an tsaron rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai da ta kunshi sojoji da ’yan sanda da ke yankin Molai a ranar Litinin.

“Bayan wani kazamin fada, an kashe soja daya wanda ba a san sunansa ba, da kuma wani ma mukamin Sajan, sai kuma wani Insifekta da ya samu rauni,” a cewar wani ganau.

Majiyarmu ta kara da cewa ’yan ta’addar sun yi awon gaba da wata motar yaki ta soji da motar daukar marasa lafiya kafin su tsere bayan isowar jiragen yaki sama na yaki.

Wani jami’in leken asiri ya shaida wa Zagazola Makama, wani kwararren masani kan yaki da ’yan ta’adda, cewa harbe-harben bindiga da aka yi a yankin a lokacin harin da aka fara da misalin karfe 6.00 na safe, ya tilasta wa mazauna kauyukan Lawanti Kura da NNPC Depot da Molai da dama guje-guje domin tsira da rayukansu.

Molai yana kan titin Maiduguri zuwa Damboa, kuma yana da nisan kilomita 10 daga birnin Maiduguri.

Harin dai ya zo ne kasa da sa’a 24 bayan da kakakin kungiyar IS Abu Umar al-Muhajir ya sanar a ranar 17 ga watan Afrilu cewa kungiyarsu za ta kaddamar da hare-hare a matsayin ramuwar gayya ga kisan shugabanta da kakakinsu da aka yi a baya-bayan nan.