✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta kashe Kwamandan Boko Haram Abu Zara da mayakansa 15 a Borno

Har yanzu ana jin karar harbe-harbe da bama-bamai a mashigar Gaizuwa.

Kungiyar ISWAP mai tayar da kayar baya a Yammacin Afirka, ta kashe wani Kwamandan Boko Haram Abu Zara da mayakansa 15 a Jihar Borno.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin na zuwa ne bayan wani kazamin fada da aka gwabza tsakanin kungiyar Boko Haram da ke yi wa kanta lakabi da kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad da kuma takwararta a Arewa maso Gabashin kasar.

A wani rahoto na Zagazola Makama, kwararre kan harkokin tsaro da ayyukan masu da’awar jihadi a yankin Tafkin Chadi, ya bayyana cewa mayakan na ISWAP karkashin jagorancin Ba’ana Chingori, sun kai wa mayakan Boko Haram hari ne a kauyen Gulmari da ke Karamar Hukumar Konduga a Jihar Borno.

Wata majiya ta ce fadan ya fara ne da harin da aka kai wa ayarin sabon Amir Jaysh na kungiyar Boko Haram, Alhaji Ali Hajja Fusam.

“Ali Fusam ya dawo ne daga sansanin Ali Ngulde da ke tsaunin Mandara inda ya karbi manyan bindigogi da babura takwas da makamai.”

Majiyar ta kara da cewa a fadan da ya barke, an kashe ’yan Boko Haram 15, an kama wata babbar bindiga yayin da shugaban na Boko Haram ya tsere.

Wata majiyar kuma a Bama ta ce har yanzu ana jin karar harbe-harbe da bama-bamai a mashigar Gaizuwa.

“A yayin da muke magana, muna jin karar harbe-harbe daga Gaizuwa.

“Mun samu labarin cewa Ali Fusam ya tsere amma an kashe mayakansa 15,” inji majiyar.