✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ISWAP ta sako ma’aikacin lafiyar da ta sace a Borno wata 11 da suka gabata

Sai dai babu cikakken bayani a kan ko an biya kudin fansa ko a'a

’Yan ta’addan ISWAP da suka yi garkuwa da wani ma’aikacin kiwon lafiya a Jihar Borno, Bulama Gaidam, kimanin watanni 11 da suka gabata a yanzu, sun sake shi.

Rahotanni sun ce ’yan ta’addan sun saki Bulama ne a garin Gubio, daga bisani kuma aka wuce da shi zuwa birnin Maiduguri domin mika shi ga iyalansa.

To sai dai kuma babu cikakken bayani ba kan ko an biya kudin fansa kafin a sako shi, ko kuma a’a.

Tun a cikin watan Maris din 2022 ne ’yan ta’addan suka kame Bulama lokacin da suka kai wani farmaki Ƙaramar Hukumar Gubio, mai tazarar kilomita 70 daga Maiduguri, kuma tun a lokacin ne yake hannunsu.

A lokacin dai, mayakan sun ce sun kai wannan farmakin ne domin su kwashi kayan abinci da man fetur daga wata motar kungiyar ayyukan jinkai a Jihar ta Borno.

Wancan farmakin dai ya tilasta wa mazauna garin arcewa daga garin domin neman tsira da rayukansu, inda sai bayan ficewar ’yan ta’addan jama’a suka koma gidajensu.