✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta sace soja da ma’akatan gwamnati

Kungiyar ta sace wani soja da ma’aikatan gwamnatin a hanyar Maiduguri.

Kungiyar ISWAP ta yi awon gaba da wani soja da ma’aikacin Gidan Gwamnatin Jihar Yobe da wasu mutum biyu.

A ranar Asabar ne mayakan ISWAP suka yi garkuwa da wasu mutum uku, ciki har da sojan mai suna Las Kofur Oyediran Adedotun a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Shi kuma ma’aikatan gidan gwamnatin ba a san inda yake ba sai bayan da a yammacin Litinin ISWAP ta fitar da hotonsa da katin shaidarsa da na sauran wadanda ta sace.

Sauran mutanen da maharan suka nuna katin shaidarsu har da wani Mustapha Lawan, ma’aikacin Hukumar Kula da Filin Jiragen Sama na Tarayya (FAAN).

Bayan an yada hotunan ne wani ma’aikacin Gidan Gwamnatin Jihar Yobe a Damaturu, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya tabbatar wa wakilinmu a ranar Talata cewa ya ga hoton daya daga cikin ma’aikatansu, Ali Shehu a ciki.

Ya ce, “Ma’aikacinmu kuma Jami’in Tuntuba na Yobe Lodge a Maiduguri, Ali Shehu wanda aka fi sani da Mai Lalle; ya bar Damaturu zuwa Maiduguri da tsakar ranar Asabar.

“Ya saba a duk lokacin da ya isa yakan kira ya sanar da mu cewa ya isa lafiya, amma a wannan karon bai yi hakan ba.

“Don haka sai muka kira ofishin na Maiduguri don tabbatar da ko ya isa, amma suka ce har yanzu bai shigo ofishin ba kuma an kira lambobin wayarsa ba sa shiga, daga nan ne muka fahimci akwai matsala.

“Abin takaici sai muka ga hotonsa da katin shaidarsa dauke da tambarin ISWAP da rubutun Larabci wanda ke nuna cewa an sace shi. Muna addu’ar Allah Ya kawo mana dauki cikin gaggawa a sako shi. ”