✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ISWAP ta yi garkuwa da matafiya a hanyar Maiduguri

Kawo yanzu ba a tantance yawan matafiyan da kungiyar ta yi awon gaba da su ba

Mayakan kungiayr ISWAP sun tare matafiya tare da yin awon gaba da su da bakin bindiga a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a ranar Asabar.

Kawo yanzu dai ba a tabbatar da adadin matafiyan da kungiyar ta yi garkuwa da su ba a harin na misalin karfe 8.30 na safiya a yankin Benisheik.

Majiyarmu ta tsaro ta ce, “Gaskiya ne an kai wa matafiya hari a safiyar nan a babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, inda wadannan mutanen suka yi awon gaba da fasinjojin da ba a san adadinsu ba a tsaksain Benishiek da Mainok; Kawo yanzu dai ba mu da bayanai sosai.”

Majiyar ta ce ce matafiyan na hanyarsu ta zuwa Maiduguri daga Damaturu ne mayakan na ISWAP suka tare su bayan sun wuce Benisheik suka tafi da su zuwa inda ba a sani ba.

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula a Yankin Arewa maso Gabas, Ambasada Ahmed Shehu, ya tabbatar da wakilinmu da labarin garkuwa da matafiyan.

“An sake garkuwa da matafiya a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri da safen nan; Me zai hana a magance wannan matsalar gaba daya?” inji shi.
Har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto babu wani bayani a hukumance game da harin.