✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP za ta kai hare-haren kunar bakin wake a Najeriya —DSS

Mayakan ISGS sun shigo daga Mali domin taimakon ISWAP a Najeriya

Hukumar tsaro ta DSS ta bankado shirin kungiyar Boko Haram da ISWAP  na kai harin kunar bakin wake a wasu al’ummomi da jami’an tsaro a Arewa Maso Gabashin Najeriya.

DSS ta ce mayakan kungiyar Jihadi ta ISGS da ke yankin Tafkin Chadi sun tsallako zuwa Najeriya domin taimaka wa ISWAP, bayan ragargazar da sojojin Rasha suka yi wa kungiyar ta ISGS a Mali.

Daraktan Hukumar DSS a Jihar Adamawa, Babagana Bulama, ya ce, “Duk da cewa an samu raguwar hare-hare saboda tsananta yakar su da hukumomin tsaro ke yi, rahotanni sun nuna ISWAP tana horas da ’yan kunar bakin wake domin kai hare-hare kan al’ummomi masu rauni da kuma jami’an tsaro.”

Bulama wanda shi ne Shugaban Daraktocin Tsaro na Jihohin Arewa Maso Gabas, ya sanar da haka ne a taronsu na wata uku-uku karo na bakwai, wanda hukumar ta shirya a Maiduguri, Jihar Borno.

Hukumar ta kira taron ne domin gano irin barazanar tsaro da yankin ke fuskanta, abin da ke haddasa su, tasirinsu da kuma hanyoyin magance su.

Ya shaida wa taron cewa, “Babban barazanar yankin ita ce ta ta’addancin kungiyar Boko Haram da ISWAP, wadanda suka yi wa yankin babban tabo ta fuskar tsaro da ci gaban rayuwa.

“Wani babban abun damuwa shi ne rahoton da muka samu na taruwar mayakan ISGS da ke yankin Takin Chadi a Najeriya bayan sojojin hayan Rasha sun fatattake su a Mali.

“Yanzu sun mayar da yankin Tafkin Chadi mafakarsu, kuma da alama so suke su hada kai da ISWAP wajen ci gaba da ayyukansu na ta’addanci,” inji shi.

Garkuwa da mutane

Ya ce bayan haka, ’yan bindiga na cin karensu babu babbaka a yankin inda suke garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a yankunan da ke da karancin ayyukan gwamnati da kuma wuraren da ke da dazuka da tsaunuka da suka mayar da su maboyarsu.

“A bincikenmu, mun gano cewa yawancin masu garkuwa da mutanen sun shigo ne daga yankin Arewa Maso Yamma, bayan jami’an tsaro sun fatattake su,” a cewarsa.

Rikicin manoma da makiyaya

Jami’in na DSS ya ce an samu raguwar rikicin manoma da makiyaya a yankin na Arewa maso Gabas a cikin wata shidan da suka gabata saboda manoma sun girbe amfanin gonarsu.

Sai dai ya ce da sauran rina a kaba, saboda akwai yiwuwar samun rikici tsakanin makiyaya da manoman rani musamman a wuraren da ke kusanci da rafuka a jihohin Adamawa da Taraba, inda ake yawan samun takun saka a tsakaninsu.

’Yan tawaye

Ya shaida wa shugabannin tsaron cewa, “Hadin gwiwar da ’yan tawayen Ambazonia na kasar Kamaro suka yi da kungiyar IPOB shi ma wani babban hadari ne.

“Taron hadin gwiwar da kungiyoyin ’yan tawayen suka yi a kasar Faransa babbar barazana ce ga jihohin Adamawa da Taraba da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya da ma Najeriya baki daya.”

Bulama ya bayyana cewa, “Rashin aiki da zaman kashe wando da matasan yankin ke yi na daga cikin abubuwan da ke sa kungiyoyin ta’addanci da sauran bata-gari suke samun saukin yaudarar matasan zuwa cikinsu.