✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Iyan Zazzau: Karfe hudu za a yi Sallar Jana’iza a Zariya

Iyan Zazzau Bashar Aminu ya rasu yana da shekara 70 sakamakon rashin lafiya

Iyalan Iyan Zazzau Alhaji Bashari Aminu sun ce za a yi masa Sallar Jana’iza bayan Sallar La’asar a Zariya.

Sun shaida wa Aminiya cewa basaraken ya rasu ne bayan zazzabin kwana daya, kuma za a yi jana’izarsa da karfe hudu na yamma ranar Juma’a 1 ga Janairu, 2020.

“Muna cikin matukar kaduwa tare da sanar da rasuwar basarake mafi karfin iko kuma dan sarki mafi tarin dukiya a Arewacin Najeriya, Iyan Zazzau Alhaji Bashir Aminu,” inji sanarwar rasuwarsa da Sarkin Zazzau na 19, Alhaji Ahmad Nuhu Bamali ya fitar a ranar Juma’a.

Allah Ya yi wa Iyan Zazzau, Alhaji Bashari Aminu rasuwa ne a daren Juma’a a Legas bayan rashin lafiyar kwana daya yana da shekara 70.

Tuni dai al’umma suka tururuwa zuwa gidan marigayin da ke Zariya domin ta’aiyyar rasuwar basaraken.

Jama’a na tururuwa a gidan marigayi domin jiran lokacin jana’iza

An haifi Iyan Zazzau Bashir Aminu ne a shekarar 1951 daga gidan Katsinawa, daya daga cikin gidajen da ke Sarautar Zazzau kuma gidan da Sarkin Zazzau na 19, marigayi Alhaji Shehu Idris ya fito.

Shi ne mai mafi yawan kuri’a daga cikin mutum uku da masu zabar Sarki a Masarautar Zazzau suka mika wa Gwamnatin Jihar Kaduna sunayensu daga cikin masu takarar kujerar bayan rasuwar marigayi Sarki Alhaji Shehu Idris a watan Satumban 2020.

Marigayi Alhaji Bashir Aminu shi ne ya shigar da kara yaan kalubalantar nadin Alhaji Ahmade Nuhu Bamalli Sarkin Zazzau na 19 a gaban kotu.

Yana neman Babbar Kotu Jihar Kaduna ta soke nadin Ahmad Bamalli, wanda ya ce ba ya daga cikin mutum ukun da Masu Zabar Sarki suka gabatar da sunayensu ga gwamnati.

Yana kuman neman bayan kotun ta soke nadin Bamalli, ta bayar da umarnin nada shi a matsayin halastaccen Sarkin Zazzau na 19 kasancewar shi ne zabin Masu Zabar Sarki a zaben da suka yi ranar 24 ga watan Satumba, 2020.

Zaben Sarkin Zazzau na 19

Idan ba a manta ba, Aminiya ta kawo rahoto cew mutum 11 da suka nemi kujerar Sarkin Zazzu bayar rasuwar Sarki na 18, Alhaji Shehu Idris.

Shi ne wanda ya yi zarra wurin samun yawa kuri’a a zaben masu neman sarautar da Mazu Zabar Sarki suka tantance suka kuma fidda mutum uku domin Gwamna El-Rufai ya nada daya a ciki.

Daga baya Gwamnan ya umarci masu zabar sarkin su sake zaben  domin ba wa karin masu namen kujerar dama, kuma a lokacin aka samu karin mutum biyu.

Bayan sake tantance ’yan takarar, sai ya masu zaben sarkin suka sake gabatar wa gwamnan da sunayen mutum ukun da suka yi zarra a farko —zabinsu bai canza ba.

Sauran ’ya’yan sarkin biyu da aka gabatar da sunayensu su ne:  Yariman Zazzau, Alhaji Muhammed Munnir Jafaru daga Gidan Bare-bari sai kuma Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris daga Gidan Katsinawa, gidan da Iyan Zazzau ya fito.

Sai dai kuma Gwaman El-Rufai ya nada Ahmad Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19, matakin da marigayin ke kalubalanta.