✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyaye sun bukaci a yi dokar da za ta amince su auri ’ya’yansu

Wani magidanci a Jihar New York ta Amurka da ke son auren ’ya’yansa da suka girma, ya kai kara don kawar da dokokin da suka…

Wani magidanci a Jihar New York ta Amurka da ke son auren ’ya’yansa da suka girma, ya kai kara don kawar da dokokin da suka hana yin aure a tsakanin muharramai, yana mai kiran hakan da batun “Cin gashin kai na mutum.”

A karar da Kotun Tarayya ta Manhattan ta yi ikirari an shigar mata ranar 1 ga Afrilu, ta ce an sakaya sunan iyayen da ke shirin neman a halasta musu auren ’ya’yan nasu saboda sun bukaci yin haka.

“Ta hanyar daurin auren, tsakanin ma’auratan duk wata dangantakar da za su iya yi da juna, za su iya samun mafi girman fahimtar juna da kusanci a tsakaninsu,” inji iyayen.

“Wannan wani bangare ne da al’umma ke kallo a matsayin abin kyama, na zamantakewar jama’a da kuma ilimin halitta,” kamar yadda takardun kotun ta sanar.

Takardun sun ba da hoto mafi kyau na wadanda za su yi sabon auren, da boye jinsinsu da shekarunsu da garinsu ko yanayin alakarsu.

“Masu neman auren sai sun manyanta,” inji rahoton.

“Wadanda za a aurar sun hada da iyayen da suka haifa na jini da ’ya’yansu.”

Ma’auratan da aka nema ba sa iya haihuwa a tare.

Wani Lauya da ke kotun bai maida martani ba game da sakonnin da ake tura masa don sharhi.

Ma’aikatar Shari’a ta birnin ta ce, har yanzu ba ta san da karar da aka shigar kan batun ba.

“Lalata tsakanin iyaye da ’ya’ya ko shakikai laifi ne na uku a karkashin dokar New York, ana iya yanke wa mutum hukuncin daurin shekara hudu a gidan yari, kuma ana daukar auren a matsayin kazanta mara kyau, yayin da matan za su fuskanci tara ko daurin wata shida a kurkuku.

A shekarar 2014, wata kotun daukaka kara a jihar ta amince da karar da ta shafi wata mata da ta auri dan uwan mahaifinta, wanda ya lura da alakar halittarta ta yi daidai da na ’yan uwanta na farko.

Amma duk da wannan hukuncin an ce yin haka wani mummunan abin tsoro ne a duniya wato aure a tsakanin iyaye da ’ya’yansu.