✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyayen Daliban Jangebe na rige-rigen tafiya da su gida

Iyayen daliba1 279 sun yi dafifi suna jira gwamnati da mika su gare su.

Iyayen dalibai mata 279 da ’yan suka sako sun yi cincirindo a garin Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara don yin tozali da ’ya’yan nasu da kuma tafiya da su gida.

Tun da sanyin safiyar Talata da labarin sakin ’yan matan ya bayyana iyaye da abokan arzikin daliban ke ta dandazo zuwa garin na Gusau.

Wani mahaifi mai suna Ibrahim ya ce ya samu labarin sakin yaran ne tun da karfe 6 na safe kun nan take ya nufi Gusau don neman ’yarsa.

Ibrahim ya ce tun da aka sace daliban kwana hudu da suka gabata bai yi barci ba saboda tsananin damuwa.

Ya kuma shaida wa Aminiya cewa ba zai koma gida ba sai kafarsa, kafar ’yarsa.

Shi ma wani wanda ’ya’yansa biyu ke cikin daliban da aka yi garkuwa da su, Hakilu Abubakar Mayanchi ya ce ya kosa gwamnati ta mika mishi ’ya’yan nashi.

Ya ce, “Abin da yi fi damu na shi ne karamar cikinsu, Aisha ta dade ba ta da lafiya.

“Tana kan shan magunguna aka sace bayan kwananta uku da komawa makaranta,” inji shi.