✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyayen daliban Kaduna na rokon a tattauna da ’yan bindiga

Sun ce amfani da karfi wurin ceto daliban na iya sa ’yan bindigar su halaka su

Iyayen dalibai 39 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da daga Kwalejin Gandun ta Tarayya (FCFM), Afaka Jihar Kaduna na rokon Gwamnati ta tatauna da masu garkuwar domin su sako ’ya’yan nasu.

Mahaifin biyu daga cikin daliban, Sani Friday, ya ce iyayen daliban na cikin tashin hankali game da matsayin daga gwamnatin jihar ta dauka na yin amfani da karfin soji wurin ceto daliban.

Ya bayyana a madadin sauran iyayen daliban cewa abin da gwamantin ke son yi na iya tunzura masu garkuwar su kashe daliban.

A hirar ta tashar Talabijin din Channels ta yi da shi ranar Alhamis, mahaifin ya ce abin da iyayen daliban da aka yi garkuwa da su ke bukata shi ne gwamnati ta tattauna da ’yan bindigar.

“Gwamnatin ce da kanta a baya ta bayyana wa al’ummar Jihar Kaduna cewa, in ta kama ta biya ’yan bindiga kudi su daina kashe mutanen jihar, zai biya su. Amma kusan shekara biyu ke nan da yin maganar.

“Mafitar da muke ganin ta fi dacewa ita ce, a fara ta hanyar tattauna. Ko da za su dauki wani mataki na tsaro, to ya kasance sai daga baya.

“Iyayen na kuka, me ya sa lokacin da hakan ta faru da mu ne muke fuskantar wannan matsalar? Idan gwamnatin jihar na ganin ba za ta tattauna da su ba, ya kamata Gwamantin Tarayya ya yi wani abu domin a dawo mana da ’ya’yanmu.”

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, bai amsa kiran wayarmu ba, balantana mu ji ta bakinsa game da wannan lamari.

Fitaccen malammin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi da ke fafutikar ganin an kawo karshe ayyukan ’yan bindiga ta hanyar tattaunawa da su da kuma yi musu afuwa ya bayyana cewa an gano wadanda suka sace daliban.