✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyayen matashin da Hukumar KASTELEA ta ‘kashe’ suna neman hakki

Akwai bukatar a bai wa iyayen Mas’ud diyya mai tsoka domin su rage radadin rashin da suka yi.

Iyayen matashin nan mai shekara 20, Mas’ud Adamu da ake zargi jami’an Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kaduna (KASTELEA) sun kashe makonni biyu da suka gabata, suna neman hakkinsu.

A wata ziyara da wakilan Trust TV suka kai gidansu marigayi Mas’ud ranar Asabar a kauyen Agursa da ke Karamar Hukumar Shira ta Jihar Bauchi, mahaifinsa Malam Adamu ya bayyana cewa ya shiga cikin damuwa tun bayan da samu labarin rasuwar dansa.

A cewarsa, na shiga cikin matsanancin hali tun bayan da na samu labarain cewa wasu jami’an Hukumar Kula Zirga-Zirgar Ababen Hawa a Jihar Kaduna sun kashe da na bayan wata ’yar sa’insa da ta shiga tsakaninsu a gefen wani titi a kwaryar birnin Kaduna.

Mahaifin ya ce jami’an na KASTELEA sun zargi direban wata Tipper da kuma dan nasa da yake masa karen mota da laifin keta dokokin tuki.

“Dana ya bar gida inda ya tafi cirani a Jihar Kaduna shekaru kadan da suka gabata, amma sai aka yi rashin sa’a ya  rasa ransa a hannun mutanen da ke ikirarin suna bai wa al’umma kariya wajen tabbatar da an kiyaye dokokin zirga-zirgar ababen hawa.

“Wannan abun takaici da me ya yi kama, don a iya sani na dana ba shi da laifi kuma yana iya kokarinsa wajen neman na abinci ta hanyar da bata saba wa doka ba.”

Mahaifiyar matashin, Karimatu Adamu, ta ce har yanzu tana cikin damuwa tun bayan da ta samu labarin kashe danta da aka yi.

Cikin zubar hawaye, ta ce duk da ba ta da ikon hukunta wadanda suka kashe shi, amma tana da tabbacin cewa Allah ba zai taba yafe wannan zalunci da aka yi wa danta ba.

“Me zan yi musu kuma, sun riga sun kashe shi, Allah ne kadai Zai yi wannan sharia saboda dana ba shi da laifi.

“Yana can yana sanaarsa ta neman halal amma maharansa suka far masa,” a cewarta.

Hakimin Kauyen Agursa, Malam Yau Haruna wanda yana daga cikin tawagar ta ziyarci Jihar Kaduna a matsayin wakilan marigayi Mas’ud bayan aukuwar lamarin, ya bayyana yadda jami’an na KASTELEA suka lakada wa matashin dukan tsiya wanda shi ne ya yi ajalinsa.

Malam Haruna ya ce bayan da suka isa Asibitin Barau Dikko da ke garin Kaduna ne likitoci sun tabbatar musu da cewa Mas’ud ya riga mu gidan gaskiya a sakamakon dukan tsiya da ya sha wanda ya raunata shi a wurare daban-daban na sassan jikinsa.

Ya ce bayan haka ne suka karbo gawarsa inda aka gudanar da jana’izarsa kuma aka binne shi a makabartar Tudun Wada da ke kan titin Bachama a Jihar Kaduna.

A wata hira da aka yi da shi ta wayar tarho, wani wakilin Mas’ud ya bayyana takaicinsa kan wannan lamari, yana mai cewa kasancewar marigayin dan asalin Jihar Bauchi, akwai bukatar gwamnoni jihohin biyu suka shiga lamarin domin ganin an yi adalci.

Ya ce akwai bukatar a bai wa iyayen Mas’ud diyya mai tsoka domin su rage radadin rashin da suka yi.