✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyayen yaran da maganin tari ya kashi sun yi watsi da diyyar Dala 1.4m

Iyayen yara nan 70 da suka mutu a kasar Gambia bayan shan wani maganin tari sun yi watsi da tayin biyan su diyyar Dala dubu…

Iyayen yara nan 70 da suka rasu a kasar Gambia bayan shan wani maganin tari sun yi watsi da tayin biyan su diyyar Dala dubu 20 a kan kowane yaro daga gwamnatin kasar.

Iyayen sun yi watsi da tayin diyyar ne bayan Ma’aikatar Mata ta Kasar  ta sanar da ware tsabar kudin har dala dubu 20 ga kowanne yaro guda don raba wa iyayen yaran 70 da nufin rage musu radadin rashin ’ya’yan nasu.

Iyayen yaran sun kuma yi watsi da tayin diyyar, wanda suka bayyana a matsayin cin mutunci a garesu.

A watan Oktoba ne yaran su 70 suka rasu ne bayan shan maganin tarin wanda kamfanin Maiden Pharmaceuticals na kasar Indiya ya sarrafa.

Kakakin iyayen yaran, Ebrima Sanyang ya ce karbiar kudaden tamkar sun bayar da kai ne biri ya hau ne game da fafutukarsu ta neman adalci wajen bin hakkin yaran da maganin tarin ya kashe.

Sun bukaci hukumar da ke kula da ingancin magunguna ta kasar ta janye ikirarinta na cewa ambaliyar ruwa ce ta yi ajalin yaran ba gurbataccen maganin ba.

Sun kuma nemi a dakatar da hukumar kula da ingancin magungunan daga duk wani bincike da ke da alaka da mutuwar yaran.