✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jadawalin Gasar Zakarun Turai ta Kakar 2020/2021

UEFA ta fitar da jadawalin ne yayin wani zama da ta yi a Geneva

Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) ta rarraba rukunan kungiyoyin da za su fafata a matakin rukuni na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai na kakar 2020/2021 ranar Alhamis.

Hukumar, a wani zaman da ta yi a birnin Geneva na kasar Switzerland, ta sanar da jerin rukunonin kungiyoyin kamar haka:

  • Rukunin A: Bayern Munich da Atletico Madrid da Red Bull Salzberg da Lokomotiv Moscow;
  • Rukunin B: Real Madrid da Shakhtar Donetsk da Inter Milan da Borussia Monchengladbach;
  • Rukunin C: FC Porto da Manchester City da Olympiakos da Marseille;
  • Rukunin D: Liverpool da Ajax da Atalanta da Midtjylland;
  • Rukunin E: Sevilla da Chelsea da Krasnodar da Rennes;
  • Rukunin F: Zenit St Petersburg da Borussia Dortmund da Lazio da Club Brugge;
  • Rukunin G: Juventus da Barcelona da Dynamo Kyiv da Ferencvaros;
  • Rukunin H: Paris Saint-Germain da Manchester United da RB Leipzig da Istanbul Basaksehir;

Za a iya cewa Liverpool ta tsinci dami a kala a rukunin da ta samu kanta a ciki idan aka yi la’akari da kananan kungiyoyin aka hada ta da su; idan aka cire Ajax ta Holland, sauran za a iya cewa ba su da wata shahara ta a zo a gani a fagen kwallon kafa.

Ita kuwa Manchester United lamarin ba haka yake ba a rukunin da ta tsinci kanta a ciki, saboda yadda ake yi wa rukunin kallon rukunin mutuwa, domin kuwa ta samu kanta a rukuni guda da kungiyar Paris Saint-Germain wacce ta kai zagayen wasan karshe a kakar bara da kuma RB Leipzig da ta kai wasan dab da na karshe.

Za a fara buga wasannin farko a ranakun 20 da 21 ga watan Oktoba; sai kuma ranar 27 da 28 na watan.