✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jagora a yaki da mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, Desmond Tutu, ya rasu

Za a rika tunawa da shi kan rawar da ya taka wajen yaki da mulkin wariyar launin fata a kasar.

Jagoran yaki da mulkin wariyar launin fata na Afirka ta Kudu, Archbishop Desmond Tutu, ya rasu yana da shekara 90.

Shugaban Kasar,  Cyril Ramaphosa, ne ya tabbatar da rasuwar tasa a cikin wata sanarwa.

Ya ce, “Rasuwar ta bude wata kofa ta alhini da jimami tare da yin bankwana da jiga-jigan da suka yi yaki wajen ’yanta Afirka ta Kudu.

Archbishop Tutu dai ya taba lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 1984, a fafutukarsa ta neman a kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar.

A matsayinsa na jigo a fafutukar kuma abokin aikin marigayi Nelson Mandela, Tutu ya taka rawar gani wajen kawo karshen mulkin tun daga 1948 har zuwa 1991.

Shugaba Ramaphosa dai ya bayyana Tutu a matsayin jagora na gari abin koyi, mai yaki da wariyar launin fata kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam.

“Mutum ne mai cike da fasaha da kwakwalwa da kuma nagarta wajen yaki da wariyar launin fata wanda ya sha fama da kalubale iri-iri a gwagwarmayar tasa,” inji Ramaphosa.