✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jama’a sun kona motar kwastam da ta kashe mutane a Jibiya

Ana takaddama tsakanin mutanen garin da Kwastam kan hatsarin motar.

Jama’ar garin Jibiya a Jihar Katsina sun kona wata motar hukumar kwastam kurmus, bayan motar ta kwace ta kashe mutum 15 a garin.

Fusatattun mutanen sun dauki matakin ne bayan faruwar lamarin a garin, amma jami’an da ke cikin motar suka ranta a na kare don tsira da rayuwarsu.

Hukumar Kwastam ta ce mutum biyar ne hatsarin ya ritsa da rayukansu a lokacin da jami’anta suka biyo wata motar da ta yi fasakwaurin shinkafa zuwa cikin garin.

Amma ganau sun ce motar ta fito ne daga hanyar Gurbi zuwa Jibiya, inda ta kwace wa direban ya hau kan mutanen da ke zaune a gefen hanya, inda mutum 10 suka rasu nan take, daga baya wasu biyar suka biyo rasu.

Wani mazaunin garin na Jibiya, Malam Lawal, ya ce mutanen sun fusata ne kan irin yadda jami’an hukumar kwastam suke gudun wuce ka’ida a cikin gari, musamman direban motar da ta yi hatsarin.

SAURARI:Yadda manyan motoci ke haddasa haddura:

A cewarsa, mutanen sun sha tsayar da shi su gargade shi amma ya ki sauraron su, ‘saboda yana ganin yana sanye da kayan sarki’.

Malam Lawal ya ce sun yi mamakin yadda hukumar ta Kwastan ta ce mutum biyar ne suka rasa rayukansa a lokacin da suka biyo wata mota shake da shinkafar da aka yi fasa-kwaurinta.

Wata majiya, hanyar Jibiya zuwa Gurbi ba hanyar masu jigilar shinkafa daga Jamhuriyar Nijar zuwa cikin garin Jibiya ba ce, ballantana har ace an biyo wani.

“Sai su zo su nuna mana yadda abin ya faru. Shin a ina mutanen da suka rasa rayukan nasu kuma wa ya kashe su?

“Wasu na cewa sun biyo wani babur ne da suke zaton ya dauko buhun shinkafa, amma dukkan bayanin da muka samu shi ne, shi mai babur din ya shigo cikin Jibiya ne ya yi sayayya zai koma kauyensu a bisa wannan babbar hanya ta zuwa Gurbi har Zamfara.

“A lokacin su kuma kawai suka dauko motarsu suka biyo shi, wanda ya zamo ba shi da zabi illa ya dawo cikin gari.

“Sannan suna da tazara mai yawa a tsakaninsu da shi har suka hau kan wadannan mutane da ke bakin titin.

“Amma kawai don son kariyar kai sai a ce mutane biyar kuma motar shinkafa aka biyo.

“To muna kalubalantar hukumar da ta fito ta nuna mana gawarwakin da kuma ita motar shinkafar.

“Yanzu haka, wani daga cikin mutanen da aka kai asibiti an shaida mana ya mutu”, inji Malam Lawal.

Har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto babu wani bayani da fito daga hukumar ’yan sandan Jihar Katsina kan lamarin.