✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kanawa sun tabbatar min cewa ni zan lashe zabe —Tinubu

An yi wa Tinubu fitar dangon-kwari a Kano a ranar Laraba.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar yana da yakinin jam’iyyar za ta kai ga nasara duba da irin fitowar dangon-kwari da magoya suka yi mata a Jihar Kano.

A ranar Talata ce dai Tinubu ya ziyarci Kano don kaddamar da yakin neman zabensa a Arewa Maso Yamma, gabanin shiga zaben Shugaban Kasa a wata mai kamawa.

Da yake jawabi ranar Laraba a filin wasa na Sani Abacha, Tinubu ya ce, “Manuniya ta nuna cewa a yakin neman zaben nan, jama’ar Kano sun san abin da ya kamata su zaba.

“Ina da yakinin goyon bayan da Gawuna da Garo ke samu zai kai jam’iyyar nan ga nasarar lashe zaben gwamna har zuwa na Shugaban Kasa,” in ji Tinubu.

Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan yadda mutane suka yi dafifi don nuna goyon bayansu ga takararsa.

A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci magoya baya da su kada wa jam’iyyar APC kuri’arsu a babban zaben da ke tafe.

Ganduje ya bai wa Tinubu tabbacin cewar kuri’ar jama’ar Kano ta APC ce duba da yadda mutane ke mararin sake ganin jam’iyyar ta mulke su.

Haka kuma, Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bukaci jama’ar yankin Arewa maso Yamma da su sake zabar APC don dorawa daga inda Shugaba Muhammadu Buhari zai tsaya.

Adamu, ya ce irin jama’ar da suka tarbi Tinubu a Kano, wata ‘yar manuniya ce da ke nuna alamar jam’iyyar za ta kai ga nasara.

Shugaban APC na kasa, ya mika tutar jam’iyyar ga dan takarar Gwamnan Jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, wanda shi ne Mataimakin Gwamnan Jihar a yanzu.

Daga cikin wadanda suka halarci taron yakin neman zaben a Kano; akwai Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu da Shettina, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato tare da gwamnonin Jihohin Arewa Maso Yamma da suka hada da Jigawa, Katsina, Zamfara, Kebbi da kuma Kaduna.