✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JAMB: Akwai yiwuwar sauya lokacin jarabawar UTME

JAMB ta ce dalibai 600,000 ne ke shan wahala wajen rajistar jarabawar.

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare (JAMB) na duba yiwuwar dage lokacin zana jarabawarta na bana.

Da farko JAMB ta shirya gudanar da jarabawar a ranar 6 zuwa 19 ga watan Yunin 2021.

Hukumar shirya jarabawar, ta tabbatar da cewa za a rubuta jarabawar gwajinta a ranar 20 ga watan Mayun 2021 bayan sauya ranar da ta yi.

Ta ce za yanke hukuncin dage jarbawar ko rubuta ta ne a ranar Juma’a bayan kammala taro tsakaninta da masu ruwa da tsaki.

Rajistran JAMB, Farfesa Ishaq Oloyode ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, yayin taron da ya yi da masu ruwa da tsaki ta intanet.

Oloyode, ya bayyana hakan a matsayin yunkurin kawo sauki ga masu yin rajistar jarabawar, duba da irin wahalar da suke sha kafin samun rajistar.

Akaluma sun nuna cewar akalla dalibai 600,000 ne suka nuna sha’awarsu ta rubuta jarabawar, amma suna fuskantar tsaiko wajen yin rajistar.