✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JAMB: Matsaloli da korafe-korafe sun dabaibaye fara jarrabawar UTME

An dai fara rubuta jarabawar ne ranar Asabar a duk fadin Najeriya.

Wasu iyaye da daliban da suka fara rubuta jarabawar UTME da Hukumar Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu (JAMB) take shiryawa sun koka kan tarin matsalolin da suka ce sun dabaibayeta a bana.

Daliban dai, a daya daga cikin cibiyoyin da aka tanada a Jihar Nasarawa sun koka da cewa karancin maganadisun na’ura wato network, tangardar su kansu na’urorin da ma canza tsarin tambayoyin da aka ce za a yi musu na ci musu tuwo a kwarya.

An dai fara rubuta jarabawar ne ranar Asabar, 19 ga watan Yunin 2021 a duk fadin Najeriya.

Sai dai a tattaunawarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Asabar, wasu daga cikin iyayen sun ce hakan na iya shafar sakamakon jarrabawar ’ya’yan nasu.

Sun yi kira ga hukumar ta JAMB kan ta tabbatar dukkan cibiyoyin da ta ware domin jarrabawar na aiki kamar yadda ya kamata domin kaucewa jefa su cikin halin ni-’ya-su.

Mista Ayuba Joshua, wani mahaifi wanda dansa ke rubuta  jarabawar ya nuna bacin ransa kan matsalolin.

“Mun zo nan tun da sanyin safiya, wasu daga cikin yaran da suka rubuta jarabawar da karfe tara sun koka kan tarin matsalolin na’urorin.

“Sun shaida mana cewa madannan kwamfutocin basa aiki yadda ya kamata, ko kuma ta yi wani abin sabanin umarnin da ake bata, har yanzu wasu daga cikinsu ma suna dakin jarrabawar saboda matsalar network din.

“To idan har yanzu ’yan karfe tara ba su fito ba, ina makomar ’yan karfe daya kenan?,” inji shi.

Kazalika, wani mahaifin mai suna Mista Chinize Nwosu ya ce, “Wadanda suka shiga jarrabawar karfe tara har kusan karfe biyu ba su fito ba.”

Ita kuwa Misis Celina Christopher kira ta yi ga JAMB da su tabbata sun samar da nagartattun tsare-tsare kafin fara jarrabawar.

Su kuwa wasu daga cikin daliban da suka yi tsokaci bisa sharadin ba za a ambaci sunansu ba sun koka kan yadda matsalar network din da ta madannai da kuma jinkirin kwamfutar ta shafi jarrabawar tasu.

“Don Allah ku taimaka ku fada wa JAMB cewa wadannan na’urorin suna da tarin matsaloli. Tun karfe tara na shiga jarrabawar, amma sai yanzu kusan karfe uku na fito,” inji daya daga cikin daliban.

A wani bangaren kuma, wasu daga cikin daliban sun yi korafin cewa tambayoyin jarrabawar ta bana sun saba da abin da hukumar ta umarcesu su karanta. (NAN)