✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JAMB ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME na 2021

Sai dai hukumar ta ce ta rike sakamakon wasu dalibai bisa zargin satar jarrabawa.

Hukumar Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) a ranar Juma’a ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME ta shekarar 2021.

An dai gudanar da jarrabawar ne tsakanin ranakun Asabar 19, zuwa Talata, 22 ga watan Yunin bana.

To sai dai hukumar, ta bakin Shugaban Sashenta na Watsa Labarai, Fabian Benjamin ta ce ta rike sakamakon wasu dalibai inda take ci gaba da bincike bisa zargin satar jarrabawa.

Ya kuma ce hukumar ba za ta yi wata-wata ba wajen janye sakamakon duk dalibin da bincike ya gano ya yi satar jarrabawar a nan gaba.

Ya shawarci daliban da su duba sakamakon ta hanyar aikewa da kalmar ‘UTMERESULT’ ta rubutaccen sako zuwa 55019 da lambar wayar da suka yi rijista da ita, inda ba da jimawa ba za a aiko musu da sakamakon.

“JAMB ta gamsu cewa amfani da Lambar Shaidar Zama dan Kasa (NIN) ya taimaka matuka wajen magance matsalar magudin jarrabawa a bana, musamman in an kwatanta da ’yan shekarun baya,” inji shi.

Sai dai ya ce duk da haka, hukumar zata je ta yi nazarin hotunan kyamarorin CCTV da ta karkafa a cibiyoyin jarrabawar domin gano wadanda suka tafka magudi.

Ko da yake har yanzu ana ci gaba da rubuta jarrabawar har zuwa nan da ranar uku ga watan Yuli, sama da dalibai miliyan daya da dubu 300 ne suka yi rijistarta a bana.