James Bond ya bukaci a watsa tokar gawarsa a ruwa | Aminiya

James Bond ya bukaci a watsa tokar gawarsa a ruwa

Sean Connery
Sean Connery

Tauraron fim din James Bond, Sean Connery, ya bar wasiya cewa idan an kona gawarsa a watsa tokar cikin teku a Scotland da kuma Bahamas.

Matar Sean Connery, Micheline Roquebrune ta ce, gurin mijinta na karshe shi ne a watsa wani kaso na tokar a kasar Bahamas da kuma kasarsa ta haihuwa, Scotland.

“Za mu maido Sean kasar kasar haihuwarsa ta Scotland saboda shi ne gurinsa na karshe; Ya bukaci a watsa tokarsa a Bahama da kuma kasarsa ta haihuwa.

“Muna da niyyar duk lokacin da damar tafiye-tafiye ta samu mu kawo shi (Scotland) kuma burinmu shi ne yin bukin tunawa da shi”, kamar yadda ta sanar da jaridar Scottish Mail.

Roquebrune, wadda ta kwashe shekara 40 tana auren Sean, ta ce za ta yi bukin ne a kusa da gidansa da ke Scotland in dokar hana zirga-zirga ba ta hana ba.

A hirar da Dansa, Jason Connery ya yi da BBC, ya ce, “Sean ya dade yana fama da rashin lafiya kafin ya rasu a Bahamas”.

Ya kuma ce ya rasu ne cikin barcinsa a gaban iyalansa, “Mutuwarsa za ta girgiza mutanen a fadin duniya”, inji shi.