✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an Hisbah sun samu horo kan damben Karate a Kano

"Dole jami'anmu su rika samun horo tunda ba makami suke rikewa ba", inji Kwamandan Hisbah.

Kungiyar masu damben Karate sun ba wa jami’an hukumar Hisbah 200 horo domin kare kansu daga bata-gari.

Wannan na dauke ne cikin wani jawabi da Shugaban Hukumar, Harun Ibn Sina ya fitar, inda ya ce dole ne jami’an nasu suke karbar irin wannan horon tunda ba sa rike makami.

“Jami’anmu dole ne su rika samun irin wannan horo tunda ba makami suke dauka ba.

“Irin wannan horo zai taimaka musu a duk lokacin da aka farmake su”, cewar Kwamandan.

'Yan Hisbah yayin da suke karbar horo
Wasu daga cikin jami’a Hisbah a lokacin da suke karbar horo.

Kwamandan ya jinjina wa kungiyar masu damben Karate reshen Jihar Kano yayin da yake karbar takardar shaidar kammala horon.

Sannan ya ce yana kyau jami’an Hisbah rika samun horon saboda gina lafiyar jikinsu.

Da yake nasa jawabin, shugaban kungiyar reshen Kano, Salisu Ibrahim, ya ce kungiyar ta ba wa hukumar takardar girmamawa ne saboda yadda take ba da hadin kai ga harkokin wasanni a jihar.

Hukumar Hisbah na daga cikin hukumomi da ba sa rike makami a Kano, kuma suna yin ayyuka da dama daga ciki har da yaki da masu yada badala a jihar.