✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’an hukumar shige da fice sun karrama Sarkin Rano

Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) Muhammad Babandede, ya bi sahun daruruwan jami’an hukumar masu ci da wadanda su ka yi ritaya da…

Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) Muhammad Babandede, ya bi sahun daruruwan jami’an hukumar masu ci da wadanda su ka yi ritaya da su ka fito daga masarautar Rano ta jihar Kano wajen karrama sabon sarki, Alhaji Kabir Muhammad Inuwa.

Bikin karramawar wanda ya gudana a fadar sarkin na Rano ranar Asabar ya kuma sami halartar tsohon mai rikon mukamin shugaban hukumar na kasa wanda kuma yanzu haka daya ne daga cikin dagattan masarautar kuma sarkin Kibiya, Alhaji Usman Umar Kibiya.

Sarkin na Rano dai wanda tsohon ma’aikacin hukumar ta shige da fice ne ya zama sarki a masarautar bayan rasuwar tsohon sarki, Alhaji Tafida Abubakar Ila.

Sarkin Kibiya da shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa su na baiwa sarkin Rano wata kyautar karramawa a fadarsa

Masarautar Rano dai na daya daga cikin wadanda gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya daga likafarsu kuma garin na da dadadden tarihi kadancewarsa daya daga cikin garuruwan Hausa bakwai.

Da ya ke jawabi yayin bikin, shugaban hukamar NIS Babandede ya bayyana sarkin a matsayin mai saukin kai, rungumar jama’a wanda kuma har yanzu ya ke ci gaba da mu’amala da hukumar har bayan ritayarsa.

Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Muhammad Babandede, sarkin Kibiya U.K. Umar tare da sarkin Rano, Alhaji Kabir Muhammad Inuwa yayin bikin karramawar

“A gurina, wannan ziyarar ’yar gida ce. A matsayina na shugaban wannan hukumar, abin alfaharina ne ganin daya daga cikin tsoffin ma’aikatanmu na rike da wannan muhimmin matsayin, saboda haka na zo taya ku murna,” inji Babandede.

Ya kara da cewa, “Na zo nan ne ba wai kawai a matsayin shugaban wannan hukumar ba, sai don ina ganin kaina a matsayin dan wannan masarautar saboda dalilai da dama.”

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, Muhammad Babandede lokacin da yake jawabi a fadar sarkin Rano

“Na farko dai a garin Rano na yi makarantar sakandire, mutumin da ya taimaka min na sami aiki a wannan hukumar (sarkin Kibiya mai ci) dan wannan masarautar me, sannan kuma babban abin sha’awar shine matata ma ‘yar nan ce.

“Saboda haka ina da alaka mai karfi da wannan masarautar. Ni da sarki aminai ne sosai kuma mun jima tare tun yana Kaigaman Rano Hakimin Kibiya.”

“Ina yi wa Allah godiya tare da taya wannan masarautar murnar samun sarki mai saukin kai da kuma kishin al’ummarsa,” inji Babandede.

Shugaban hukumar ya kuma yabawa masu shirya taron tare da shawartar ragowar jami’an hukumar kan su yi koyi da sarkin.

Ni na fi kowa farin ciki – Sarkin Kibiya

Shi ma da ya ke nasa jawabin, sarkin Kibiya, Alhaji Usman Umar Kibiya ya ce ya fi kowa farin ciki da karramawar kasancewar shine ya yi silar sarkin da ma shugaban hukumar shige da ficen mai ci su ka sami aiki da hukumar.

A cewarsa, “Yau farin cikina ba zai misaltu ba kasancewar mutanen da na samarwa aiki ba su bani kunya ba.

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, Muhammad Babandede lokacin da yake jawabi a fadar sarkin Rano

“Ban taba tsammanin za su kai matsayin da su ke kai ba yanzu, su na iya bakin kokarinsu, saboda haka Alhamdulillah ba na da-na-sanin daukarsu.”

“Wannan karramawar tamu ce baki daya,” inji sarkin na Kibiya.

Daga nan sai ya yi kira ga ragowar matasa da su ma su yi koyi da kyawawan halayen sarkin.

Da ya ke mayar da jawabi, sarkin na Rano, Alhaji Kabir Muhammad Inuwa ya bayyana bikin a matsayin na tarihi kuma mai sosa zuciya sannan ya godewa shugaban hukumar kan kyakkyawar alakarsa da masarautar.

Ya godewa wadanda su ka shirya taron musamman sarkin Kibiya saboda yin silar samun aikinsa a hukumar.

“Ni a kan kaina ina ganin wannan karramawar gaba dayanta ta tsohon shugaban hukumar ce kuma sarkin Kibiya, na tabbatar yau ya fi kowa farin ciki,” inji sarki Kabir.

Bikin karramawar ya kuma sami halartar kwamandojin hukumar na jihohin Kano da Jigawa, shugaban makarantar horar da jami’an hukumar da ke Kano, shugabannin kananan hukumomin Rano da Kibiya da ma sauran hakiman masarautar.