✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an Kwastam sun bude wa mutane wuta a Katsina

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake zarginsu da yunkurin hallaka mutane a Jihar ba.

A ranar Juma’a ne wasu jami’a da ake zargin na hukumar Kwastan ne suka yi harbin kan mai uwa da wabi a garin Fadi-Gurje na Karamar Hukumar Mani a Jihar Katsina.

Rahotanni sun ce jami’an sun shigo garin ne da ke kan hanyar Katsina zuwa Daura sannan ba su yi wata-wata ba suka fara harbin, wanda ya janyo suka sami wani mai suna Auwal Sani mai kimanin shekaru 34 a kafa.

A cewar jama’ar garin, ba su ga wasu masu dauke da kayan laifin da suka shigo garin ba, balle a ce su suka biyo.

Wani mazaunin yankin ya shida wa Aminiya cewa hakan ya sa jama’ar gari ranta a na kare don tsira da rayuwarsu, har suka gama suka fita ba a san inda suka yi ba.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake zargin jami’an hukumar ta Kwatsam da yin harbi kan jama’a ba.

Ko a kwanakin baya sai da hatta Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari ya koka kan yadda suke kashe jama’a, maimakon su kare su.

Kazalika, a kwanakin baya, sai da wadannan jami’ai suka yi sanadiyar mutuwar mutum 15 a Karamar Hukumar Jibiya, sannan kuma suka bude wuta kan motar tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, kuma Kwamishinan Kananan Jukumomi, Ya’u Umar Gwajogwajo.

Hakan dai ya sa jama’a jefa alamomin tambaya kan yadda hukumar ke gudanar da aikinta a Jihar, wacce ita ce Jihar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, sabanin yadda take a wasu Jihohin.

Sai dai duk yunkurin wakilinmu na ji daga bakin hukumar a Jihar ta Katsina ya ci tura, ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Amma Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace, tuni aka kai wanda aka harba din asibitin kashi da ke cikin garin Katsina domin yi masa magani.

Kakakin ya kara da cewa, tuni Kwamishinan ’yan sandan Jihar, CP Sanusi Buba ya tabbatarwa da jama’ar garin tabbacin samar masu tsaro inda ya bukaci da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

SP Gambo ya kuma ce hukumar ta dukufa wajen binciko masu hannu a lamarin don su fuskanci fishin hukuma.