✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Jami’an Kwastam sun kashe ’yan Jibiya 25 a shekara 3’

Dan Majalisar ya ce yanzu haka mutanen yankin ba sa farin ciki da hukumar.

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Jibiya da Kaita, Hon. Sada Soli ya ce jami’an Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Kasa (NCS) sun kashe akalla mazauna Jibiya 25 a cikin shekara uku.

Hon. Sada ya bayyana hakan ne ranar Litinin lokacin da yake tare da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari domin karbar wakilcin hukumar da suka zo Jihar kan kisan da wata motarsu ta sintiri ta yi wa mutanen garin a makon da ya gabata.

Dan Majalisar ya ce yanzu haka mutanen garin ba sa farin ciki da hukumar.

“Sam ba ma farin ciki da yadda jami’an hukumar suke tafiyar da al’amuransu a yankin.

“A cikin shekara uku kawai, muna da alkaluman cewa an kashe mutum 25, amma wannan ne karon farko da batun yake daukar hankali sosai,” inji shi.

Tura ta kai bango – Kungiyoyin Fararen Hula

A nasu bangaren kuwa, Kungiyoyin Fararen Hula (CSOs) a Jihar, wadanda Bashir Ruwan Godiya ya wakilta sun ce ba za su ci gaba da lamuntar salon jami’an hukumar a Jiharsu ba.

“Babu wani dalili kowanne iri ne da zai sa wanda aka ba horo ya kare rayukan jama’a zai koma kashe su saboda Shinkafa.

“Ko malala gashin tinkiya za ku tara wa gwamnati in dai za ku kashe ko da rai daya ne to bata da amfani.

“An jima ana kashe mana mutane kuma ba a daukar kowanne irin mataki,” inji Bashir.

Tun da farko da yake jawabi a madadin hukumar, Mataimakin Babban Kwantirola (ACG) Uba Muhammad ya ce sun je Jihar ne da nufin jajanta musu da kuma tattaunawa da mutanen da abin ya faru don gano yawan barnar da aka yi sannan su kai rahoto ga shalkwatarsu ta kasa.

A biya diyya, a hukunta masu laifi ko mu hadu a kotu – Masari

Shi kuwa Gwamna Masari ya shaida wa tawagar wacce Babban Kwantirolan hukumar na kasa ya kafa cewa ya zama wajibi a hukunta masu hannu a ciki sannan a biya iyalan wadanda lamarin ya shafa diyya.

Ya ce muddin aka ki yin hakan, Jihar ba ta da wani zabi face ta dauki matakin shari’a a kan hukumar.

“Ku mika sakonmu kai tsaye ga Shugaban hukumarku cewa bukatarmu a bayyane take; dole a biya diyya ga wadanda aka kashe da wadanda aka ji wa raunuka sannan a hukunta masu hannu a ciki. Kin yin hakan zai sa mu dauki matakin shari’a. Ba lallai ne mu yi nasara ba, amma za mu jarraba,” inji Gwamna Masari.