✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an kwastam sun nuna wa Gwamnan Katsina yatsa

Sun bude wa kwamishina wuta bayan takaddamar kashe mutane a Jibiaya

Jami’an hukumar kwastam sun bude wuta a kan ayarin motocin Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu kuma tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Ya’u Umar Gwajogwajo, a hanyarsa ta zuwa mahaifarsa, garin Mai’aduwa.

Lamarin ya faru ne kasa da wata guda bayan wata sa-toka-sa-katsi kan kisan mutum 15 da jami’an kwastam suka yi ta hanyar tukin ganganci a garin Jibiya, wanda Gwamnan Katsina, Aminu Masari ya ce dole hukumar ta hukunta masu laifin ta kuma biya diyya ga iyalan mamatan, in ba haka ba gwamnatin jihar za ta maka hukumar a gaban kuliya.

A safiyar Talata kuma, wasu jami’an suka bude wa motococin kwamishinan jihar wauta a hanyarsa ta zuwa Mai’adua daga Daura.

Wani wanda ya nemi da a sakaya sunan shi ya ce, “Wannan cin fuska ne ga al’ummar jihar baki daya kuma nuna yatsa ne ga shi Gwamnan a kan cewa ya je duk irin matakin da zai dauka ya dauka.

“Kuma mu muna kallon wannan lamarin tamkar yunkurin hallaka wani, domin dai zai yi wuya ko da wannan rana aka kawo wadannan jami’ai a ce ba za su iya tantance motocin masu laifi ba, balle kuma a ce ayari ne wanda ya fito daga Daura zuwa Mai’aduwa, ba wai daga Kongolon suka fito ba balle a ce ana zargin su.

“Kuma shin ba su da wata hanya ta tsayar da motoci sai ta yin amfani da bindiga?”

Mai maganar ya kara da cewa, dama ba tun yanzu ba jami’an suke aiwatar da irin wannan mummunan aikin.

Sai kuma ya ce, “Hakika laifi ne yin fasakwauri”, amma kuma ya tsaya kai da fata cewa, “Ai duk motocin da ake yin amfani da su an san su”.

– Ba farau ba

A kwanakin baya ne, bayan jami’an kwastam sun yi sanadiyyar mutuwar mutum akalla 15 a garin Jibiya, Gwamna Masari ya harzuka, har ya yi barazanar gurfanar da hukumar a gaban kuliya muddin ba ta hukunta jami’an da ke da hannu a kisan ba ta kuma biya diyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ba.

Matakin da ya dauka ya yi sanadiyyar turo wata tawaga daga hedikwatar hukumar ta kasa domin jajantawa tare da yin ta’aziyya ga gwamnati da iyalan wadanda suka rasa rayukan nasu.

‘Kwastam na neman cire katsinawa da Najeriya’

A lokacin ziyarar ta’aziyyar, Masari ya tunatar da jami’an a kan irin yadda suka kama wata motar gwamnatin jihar mai kuma dauke da lamba da tambarin gwamnatin jihar, sai da aka kai ruwa rana kafin su saki motar.

Kazalika, duk da ya nuna ba ya goyon bayan yin fasakwauri, ya ce yana da kyau jami’an hukumar su rika mutunta doka da kuma ka’idodin aikinsu.

A cewarsa, jami’an suna daf da fitar da wasu yankunan jihar daga Najeriya ta hanyar hana su yin amfani da wasu kayan da doka ta yardar masu yin amfani da su a matsayinsu na ’yan kasa.

An kama masu lafin —Hukumar kwastam

A nata bangaren, hukumar kwastan din ta kira wani taron manema labarai ranar Laraba, inda ta tabbatar da faruwar lamarin.

Mukaddashin Kwantarola, DC Dalha Wada Chedi ya ce, tuni wadanda suka aikata wancan laifi suna hannu, har an kafa kwamitin bincike domin gano dalilin faruwar hakan, wanda ya ce hukumar ba ta ji dadi ba.

A karshe DC Dalha ya bayyana irin nasarorin da hukumar ta samu na kama kayan milyoyin nairori da aka yi fasakwaurinsu zuwa Najeriya ta shiyyar.