✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an shige da fice a Katsina ba su iya ko fareti ba —Babandede

Shugaban Hukumar ya ce har masauki jami'ai ke bin bakin haure suna karbar rashawa.

Kwamturola-Janar na Hukumar Shige ta Fice ta Najeriya, Muhammad Babandede, ya ce zai sauya wa jami’anta na shiyyar Katsina wuraren aiki, saboda yawan karbar rashawa.

Babandede, wanda ya ziyarci Shiyyar ranar Litinin, ya ce jami’an Shiyyar ba su iya ko fareti ba, amma har masauki suke bin bakin haure su karbi cin hanci.

“Yawancinku kun ma san inda bakin hauren suke, kuna zuwa wurinsu ku karbi kudi; To a hir dinku! Saboda haka zan wargaza Shiyyar Katsina, in sauya muku wuraren aiki.

“Na lura dadewar da wadansunku suka yi a nan fiye da kima ce ta haifar da wannan matsalar,” inji shi.

A jawabinsa ga jami’an Shiyyar, Babandede ya nuna fushinsa kan rashin iya faretinsu, amma, “Na sha samun rahoto kan shingayen binciken da kuke karbar kudade.

“Ban san wa kuke ba wa kudaden ba, domin dai a Abuja ban taba sanin ana tura kudade daga nan ba.

“Zan bincika, shin Kodinetan Shiyya ne ko Konturola-Konturola ne suke amsar kudaden. Idan [a cikinsu] da mai ba ku umarnin [karbar kudade]  ku yi bayani.”

Kwamturola-Janar din ya kara da cewa duk jami’in da aka sauya wa wurin aiki daga Katsina ya nemi kamun kafa, to a bakin aikinsa.

“Na san me ke faruwa, amma tunda na sha yi muku magana na kuma ba da umarni kun yi kunnen kashi, to zan sauya muku wuraren aiki; Ku je ku yi kamun kafa.

“Na san wadansunku za su je wurin wasu [manya] su roka cewa kar a sauya musu wurarin aiki. To duk wanda ya yi haka to a bakin aikinsa.”

Ya ce ya ziyarci Jihar Katsina ce domin aiki tare da sarakunan gargajiya wajen gano bakin haure a wani bangare na rage matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

“Matsalar tsaro a kasar nan ta yi yawa, shi ya sa na zo Katsina domin aiki tare da sarakunan gargajiya wajen zakulo bakin haure a lokacin da suke shigowa da kuma wadanda suke zama a Najeriya.

“Hakan ba zai yiwu ba muddin ku ma’aikatana ba ku da da’a, kuna karbar cin hanci ko ‘haraji’ a hannun mutane a kan iyakoki.

“Ba za ta sabu ba, kasarmu ba za ta ci gaba ba muddin muka mayar da rashawa wani bangare na rayuwarmu.

“Sai mun kawar da ita za mu samu nasara, amma kuma ban ga alamar da’a a tare da ku ba,” inji shi.

Jihar Katsina daya ce daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da matsalar tsaro ta ’yan bindiga ta fi ci wa tuwo a kwarya.

A lokuta da dama an sha alakanata matsalar makamai a hannun mutane ba bisa ka’ida ba da karakainar bakin haure.