✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro na taimakon masu fasakwaurin ma’adinai —Minista

Ministan Ma'adinai ya ce masu satar ma'adinai na amfani da jiragen alfarma.

Minista a Ma’aikatar Ma’adinai, Uche Ogah, ya bukaci Majalisar Dattawa ta yi dokar yanke wa masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba hukuncin kisa.

Ogah ya ce Najeriya na asarar Dala biliyan tara a duk shekara a dalilin ayyukan masu hakar zinare ba bisa ka’ida ba, sannan kuma masu fasakwaurin zinare a Najeriya suna amfani ne da jiragen kashin kai.

  1. An kashe jagoran ISWAP, Abu Mus’ab Al-Barnawi
  2. Me Ake Yi Da Kudaden Harajin Da Ake Karba?

“Yawancin masu fasakwaurin zinare a Najeriya suna amfani ne da jiragen kashin kai, shi ya sa ya kamata a hade batun mallakar jiragen kashin kai a Najeriya a wuri daya,” inji shi.

Ya shaida wa Kwamitin Ma’adinai na Majalisar Dattawa da ke bincike kan lamarin cewa jami’an tsaro da al’ummomin yankunan da ake hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba suna taimaka wa masu masu fasakwaurin zinare.

Ministan ya bayyana cewa hadin bakin da sauran bangaorin ke yi da masu fasakwauri da hakar zinare ba bisa ka’ida ba ne ya sa ayyukan bata-garin ke ci gaba.

“Idan har so ake a magance wannan matsala yadda ya kamata, to dole sai an yi tsauran dokokin hukumta masu laifin,” inji shi.

A cewarsa, daga cikin hanyoyin, za a iya kafa ’yan sandan tsaron ma’adinai da kotunan hukuta masu laifin da kuma wadatar da ma’aikatar da kudade da kayan aiki, sai kuma wayar da kan jama’ar kasa kan illar hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

A jawabinsa, Shugaban Kwamitin, Sanata Umar Tanko Al-Makura, ya ce kwamitin zai gayyato shugabannin hukumomin da suka dace domin amsa tambayoyi.

Hukumomin da ya lissafa cewa shugabanninsu za su amsa tambayoyi sun hada da Babban Bankin Najeriya(CBN), Hukumar Kwastam da Hukumar Shiga da Fice.

Sauran sun hada da Hukumar tsaro ta DSS da hukumar EFCC da Rundundar ’Yan Sandan Najeriya da kuma Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwan( NPA).